--
Albishir Mai dadi ga wadanda suka nemi aikin (Police) Hukunar 'Yan Sanda ta Fitar da sabuwar sanarwa

Albishir Mai dadi ga wadanda suka nemi aikin (Police) Hukunar 'Yan Sanda ta Fitar da sabuwar sanarwa


SANARWA GA MASU NEMAN SHIGA AIKIN 'YAN SANDA


Hukumar kula da aikin 'yan sandan Nigeria Police Service Commission (PSC) tana sanar da jama'a musamman wadanda suka nemi shiga aikin 'yan sanda suka rubuta exam a watan 10 da ya wuce, cewa ta karbi rahoton sakamakon jarrabawa daga Mataimakin Supeta Janar na 'yan sanda wanda yake lura da bangaren horon aikin 'yan sanda (DIG Training) Danmallam Muhammad


Matasa maza da mata mutum dubu 74 da 58 suka zauna suka rubuta jarrabawan a jihohin tarayyar Nigeria 36 da birnin tarayya Abuja, yawan maza dubu 62 da dari 588, yawan mata da suka rubuta jarrabawan dubu 11 da dari 470, cikin mutum sama da dubu 74 mutum dubu 10 za'a dauka


Hukumar PSC tana sanar da matasan cewa wadanda suka samu nasaran cin jarrabawa za'a kirasu zuwa gwajin lafiya nan da kwanaki 10 masu zuwa, wato ranar 22-11-2021 wanda zai gudana a Zonal Headquarters guda 17 da ake dasu a fadin Nigeria


Wannan sanarwan ya fito yau juma'a 12-11-2021 daga jami'in yada labarai da hulda da jama'a na hukumar kula da aikin 'yan sanda (PSC) Mr Ikechukwu Ani


Karin bayani:

Duk wanda ya san ya rubuta jarrabawan neman shiga aikin 'yan sanda ya kasance mai yawan duba sakon email da SMS, wanda yaci jarrabawa za'a kirashi gwajin lafiya wanda za'a fara nan da kwanaki 10 masu zuwa


Za'a fitar da sakamakon karshe a watan 12 December, kuma za'a fara bada horo training a watan 12


Muna fatan Allah Ya bawa mai rabo sa'a


Arewa Intelligence 

12-11-2021

0 Response to "Albishir Mai dadi ga wadanda suka nemi aikin (Police) Hukunar 'Yan Sanda ta Fitar da sabuwar sanarwa"

Post a Comment