--
Babu wata Kyautar Data ko Airtime Daga Mawaki Davido Karyane Ncc Tayi Gargadi Ga 'Yan Najeriya Duba Abinda Tace

Babu wata Kyautar Data ko Airtime Daga Mawaki Davido Karyane Ncc Tayi Gargadi Ga 'Yan Najeriya Duba Abinda Tace


NCC ta ƙaryata rabon katin waya da data da ga Davido


Hukumar Kula da Harkokin Sadarwa ta Ƙasa, NCC ta yi gargaɗi a kan tallan da a ke yaɗawa a kafafen sadarwa cewa fitaccen mawaƙin nan David Adeleke, wanda a ka fi sani da Davido ya na raba katin waya da data kyauta.


Jami'in Hulɗa da Jama'a na hukumar, Dakta Ikechukwu Adinde ne ya yi gargaɗin a wata sanarwa da ya fitar a yau Talata a Abuja.


"A kwai wasu gungun ƴan damfara da su ke yaɗa talala mai taken "Rabon katin waya da data na Davido."


Ya ƙara da cewa tallan, wanda ya yaɗu a kafafen sadarwa, na cewa wai Davido na rabon katin waya na 5,000 da kuma data mai nauyin giga 10,000 kyauta a kowanne layin sadarwa domin murnar zagayowar ranar haihuwarsa.


Ya ce NCC ce ta gano gungun ƴan damfarar a binciken ta da ta saba yi na kafafen sadarwa, inda ta gano ɓata-garin da su ke shirin cutar al'umma.


Adinde ya ƙara da cewa tallan ya shafi miliyoyin ƴan Nijeriya bayan da ƴan damfarar su ka yi amfani da yawan kyautar da Davido ke yi su ka fara zaluntar jama'a.


Adinde ya ce hukumar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen wayar da kan ƴan ƙasa masu amfani da hanyoyin sadarwa wajen ba su muhimman bayanai domin kare su daga ƴan damfara.

0 Response to "Babu wata Kyautar Data ko Airtime Daga Mawaki Davido Karyane Ncc Tayi Gargadi Ga 'Yan Najeriya Duba Abinda Tace"

Post a Comment