--
Idan antura maka sakon gayyatar Training baka samu halarta ba,  duba abinda ka iya samunka gameda tsarin NYIF Na Gwamnatin Tarayya

Idan antura maka sakon gayyatar Training baka samu halarta ba, duba abinda ka iya samunka gameda tsarin NYIF Na Gwamnatin Tarayya


Shirin asusun saka jarin matasa najeriya 

#NYIF dole ne mai cin gajiyar shirin sai ya samu horo za'a amince da rancen sa, mutukar ka samu sakon karbar horo sai wani uzirin ya hanaka halartar horon ( TRAINING ) toh zasu kara baka dama yayin da zasu kara turo maka da sakon ta Email address naka cewa ka rubuta musu dalilin daya hana ka samun halartar horon.bayan ka aika musu da amsoshin da sukayi maka kai ma kana cikin wanda zaa amince da rancen su.


Asusun saka jari matasan yana bayar da dama ga wanda suka sanya student account ma'ana karamin asusun ajiya wanda bai daukar kudi masu yawa #NYIF zasu tura maka da sako cewa ka ziyarce bankin ka don mayar da asusun ajiyar ka babba,bayan ka mayar dashi lokaci yana yi zasu sakar maka kudin ka,ba kamar Covid-19 loan tcf ba. wanda koda kaje ka mayar da asusun ajiyar ka babba sai kayi sa'ar gaske ko sai kabi hanyoyin sannan za'a sakar maka kudin naka.


Nayi imani da Allah cewa duk wanda suka nemi wannan rance na asusun saka jarin matasa najeriya NYIF har suka samu sakon Pre-quiafuly a SMS nasu suka samu damar shigar da bayanin kasuwanci su toh zasu amfana da wannan tallafi ganin cewa wannan tsarin shugaban kasa Muhammadu buhari ya fitar da 75Billon don mu matasa yayin da wanda basu da rijistar kamfani zasu samu 250k masu rijistar kamfani 300k.


Cikin N75Billon da shugaban kasa ya fitar an kashe Naira N12.5Billion ga wanda suka ci gajiyar shirin A,B, ga batche C ana gudanarwa yanzu haka inada karbar horon yayi nesa saura kiris a kammala, bayan an kammala zaa kara fitar da wasu sunayen da zaa basu horo nan bada jimawa ba ba. Mu cigaba da duba imel dinmu akai-akai. 


©Ahmed El-rufai Idris 💪🙋

0 Response to "Idan antura maka sakon gayyatar Training baka samu halarta ba, duba abinda ka iya samunka gameda tsarin NYIF Na Gwamnatin Tarayya"

Post a Comment