--
Kalli bidiyon Fusataccen Kostoman Banki ya hana kowa sakat acikin Banki kan matsalar BVN

Kalli bidiyon Fusataccen Kostoman Banki ya hana kowa sakat acikin Banki kan matsalar BVN


Watakila ya gaji da hidimar su, wani dan Najeriya ya kutsa kai bankinsa domin ya bayyana ra’ayinsa na yanke hulda da su.


Mutumin da ya fusata ya hargitsa lamurra yayin da ya yi ihu da babbar murya cewa a rufe asusunsa.


A cikin wani dan gajeren bidiyon da @instablog9ja ya yada a Instagram, ana iya jin mutumin yana gunaguni game da batun BVN kuma ya fusata da kururuwa tare da cewa 'aikin banza'. 


Kamar dai ba komai ba, sai ya matso kusa da ma'aikaciyar bankin ya bayyana mata bukatar a ta rufe asusun. 


Duk wani kokarin da ma’aikatan bankin suka yi na kwantar masa da hankali bai yi nasara ba.


 Kalli Bidiyon A kasa: 



0 Response to "Kalli bidiyon Fusataccen Kostoman Banki ya hana kowa sakat acikin Banki kan matsalar BVN"

Post a Comment