--
Labari mai Dadi Ga duk wanda yasan ya cike Tallafin AGMIES LOAN,  FMRD,  SPW,  RRR CODE,  Covid-19,  NYIF, NYFB, Suvival Fund, N-power,  Trader Moni, Ka kasance Cikin Shiri Daga Yanzu Kowanne Lokaci Duba Wannan Sanarwar da aka fitar Yanzu

Labari mai Dadi Ga duk wanda yasan ya cike Tallafin AGMIES LOAN, FMRD, SPW, RRR CODE, Covid-19, NYIF, NYFB, Suvival Fund, N-power, Trader Moni, Ka kasance Cikin Shiri Daga Yanzu Kowanne Lokaci Duba Wannan Sanarwar da aka fitar Yanzu


GA WASU LABARAI DA TINATARWA MASU DADI GA MASU CIKE TSARE TSAREN GWAMNATIN TARAYYA DOMIN NEMAN TALLAFI KO BASHI.


N-POWER, Kowanne lokaci daga yanzu zuwa Karshen Satinnan  Wadanda suke jiran albashinsu na N-Power zasu gani Kamar yadda Hukumar dake kula da Shirin ta sanar.



SPW. Dukkan Mutanan da Suka shiga tsarin Special public works Wadanda ba'a biyasuba adalilin MATSALOLI Daya Shafi account dinsu ko matsala me kama da Haka zasu iya ganin kudinsu gaba Daya kafin karshen shekarar Nan, Kuma ma'aikatar kudi  zata saki kudin kafin karshen watannan da muke ciki inji karamin ministan kwadagi festus Kiyamo.


FMRD  Tsarin bada tallafin noma Wanda aka Fara biyan mutane kudadan tallafi zai cigaba da gudana INDA za'a cigaba da biyan Wadanda aka tantance bayanansu.



NYIF. Mutane dubu goman da aka fitar da sunayansu akarkashin wannan shirin suna GAF da karbar sakon training dinsu ko Kuma ganin kudadansu Kai tsaye ta cikin account dinsu matukar baida matsala akansa.


SURVIVAL FUND. Masu jiran sake bude wannan Shirin karsu fidda Rai domin har yanzu akwai labarin sake budeshi domin sababbin mutane masu applying,  Amma ko an bude Dole sai kanada CAC TIN NUMBER da SMEDAN NUMBER  Dan Haka azama cikin Shiri.


RRR CODE. Tsarin da aka cike watannin baya yanzu Haka Ana Cigaba da biyan Wasu daga cikin Wadanda Suka shiga Shirin awasu JIHOHI, Kaima idan Ka TABBATAR ka cike Shirin kajira ananan zuwa kanka ko JIHARKA.


GA KUMA TSARE TSAREN DA HAR YANZU AKE KAN CIKESU.


COVID 19 LOAN NON INTERESTEST. Har yanzu Yana bude, Wanda Yake da CAC zai iya cikeshi Wanda bashi da CAC zai iya cikeshi.



AGMIES LOAN NON INTERESTEST. Shima Wannan tsarin ananan Ana cikeshi, Amma sai kanada EDI certificate da Business plan da sauran bayanai da Suka shafeka.


NYIF. Yanzu Haka Ana Saban applying na wannan tsarin, Amma Wanda Shekarunsa Suka wuce 35 Babu shi aciki, Sannan Wanda ya cike abaya koya samu ko bai samuba Babu shi aciki.



TREADERMONI. Yanzu Haka shima Wannan Shirin Yana cigaba da tafiya ako Ina AFADIN NIGERIA Kuma Nan kusa za'a Sami abinda aka nema, Amma gaskiyar magana layin glo da 9mobile yafi tafiya a tsarin, Bance ragowar basayiba Amma Wadanda na ambata sunfi tafiya. Ga code din shiga Shirin, *4255*21# Ina bada shawara kuyi gaggawar shiga Shirin.


Dukkan Wanda ya shiga Daya daga cikin shirye shiryennan Dana ambata da Wanda zai shiga anan gaba Ina rokon ALLAH YASA dukkanmu mudace.

0 Response to "Labari mai Dadi Ga duk wanda yasan ya cike Tallafin AGMIES LOAN, FMRD, SPW, RRR CODE, Covid-19, NYIF, NYFB, Suvival Fund, N-power, Trader Moni, Ka kasance Cikin Shiri Daga Yanzu Kowanne Lokaci Duba Wannan Sanarwar da aka fitar Yanzu"

Post a Comment