--
MTN sun cire masa N50 ta Caller Tune ya kaisu kara Kotu Anbiyashi tarar N5.5M kalli bidiyon Zaman kotun

MTN sun cire masa N50 ta Caller Tune ya kaisu kara Kotu Anbiyashi tarar N5.5M kalli bidiyon Zaman kotun


Wani dan Najeriya mai suna Emmanuel Anenih a watan Oktoban 2014, ya maka kamfanin sadarwa na MTN a gaban kotu kan cire masa naira hamsin da aka yi kuma aka saka masa wakar kira duk da bai bukata ba. 


Kamar yadda shafin @naija_reporter suka ruwaito, bayan fafatawa da aka yi tsakanin Emmanuel na kamfanin MTN, ya samu galaba a shari'ar inda kotu ta umarci MTN da ta biya shi makuden kudi. 


A yadda ta kaya a kotun, bayan da alkali ya tabbatar da samun shaidu gamsassu cewa an cutar da shi, an yankewa kamfanin sadarwa na MTN hukunci. A wata wasika da MTN ta tura wa wanda yayi kara, ta aminta cewa ta kwashe masa kudin inda ta saka masa wakar da mai kiransa zai ji duk da bai bukata ba. 


Amma kuma daga bisani, ta tura masa kyautar N700 na kira ga wanda yayi kara kan shekaru takwas da yayi yana amfani da layinsa bayan yayi korafin. Babban alkalin kotun, Mai shari'a Ishaq Bello a hukuncinsa, ya ce dari bakwan da aka tura masa bata kai diyyar katsewa mai karar jin dadinsa da aka yi ba. 


Kotun daga nan ta umarci kamfanin sadarwa na MTN da ta biya shi naira miliyan biyar na barnar da ta yi masa wurin katse masa zaman lumanarsa ta hanyar saka masa wakar da masu kira za su ji ba tare da ya bukata ba. Har ila yau, kotun ta bukaci kamfanin sadarwa na MTN da ta kara masa naira dubu dari biyar na kudaden da ya kashe wurin shari'a. 


Kalli bidiyon akasa:


0 Response to "MTN sun cire masa N50 ta Caller Tune ya kaisu kara Kotu Anbiyashi tarar N5.5M kalli bidiyon Zaman kotun"

Post a Comment