--
Nazir Sarkin waka ya sake fito da hujjar Tafsirin Ayar da ta fadi cewa a daki Mace a Alkur’ani

Nazir Sarkin waka ya sake fito da hujjar Tafsirin Ayar da ta fadi cewa a daki Mace a Alkur’ani


A jiya ne wani cece-kuce tare da martani kala-kala ya kaure a shafin sada zumunta Istagram na Ficaccan Mawaki Naziru M Ahmad wanda aka fi sani da Sarkin waka.


Akan wata bidiyo ta ya wallafa a shafin nasa da Jama’a suke ganin kamar yace ya halatta idan mace tayiwa Mijin ta laifi ya daje ta, wanda Jama’a suka yi ta yamudidi da zancen.


To a yau kuma Mawaki Nazir M Ahmad wato Sarkin waka ya sake fito da hujjar tafsirin ayar da tace a daki mace a Alkur’ani.


Naziru Sarkin Waka ba cewa ya yi a daki mata ba kuma ba da’awa yake yi akan a daki mata ba kuma ko a yadda Ayar ta zo wadanne irin mata aka ce a daka ne?, Me ya hada macen kirki wacce ta ke zaune da mijin ta lafiya da tayar da jijiyar wuyar an ce a daki mata?.


Kafin ayi dukan me sauran Ayoyin surar su ka ce ayi ne a matsayin ladabtarwa kamin a kai ga dukan?, Sannan wane irin duka? Kuma ta wace siga? Ba fa akan ma’ana ko fassarar Aya ake magana ba.


Shi fa Naziru Sarkin martani yake yiwa wasu mata (‘Yan Feminist) da suka ce babu in da a cikin Alƙur’ani Allah ya ce a daki mata, Shine fa Naziru Sarkin waka ya kawo musu Ayar ya nemi suma su kawo wacce tace kar a daki matan Shikenan fa.


Karyata Ayar Alkur’ani suka yi fa a kaikaice, shi kuma ya kawo Ayar tare da kalubalantar su akan samuwar ta bayan sun ce babu ita.


Ga cikekkiyar bidiyon nan domin ku kalla.



0 Response to "Nazir Sarkin waka ya sake fito da hujjar Tafsirin Ayar da ta fadi cewa a daki Mace a Alkur’ani"

Post a Comment