--
An kama wani mutum da matar abokinsa suna tafka lalata a marabar Jos Kaduna

An kama wani mutum da matar abokinsa suna tafka lalata a marabar Jos Kaduna


 

Dubu ya cima, An kama wani magidanci da matar aure a maraban jos Kaduna cikin daki guda suna lalata. 

Bisani an kama shine lokacin da ya tura matanshi su biyu gidan iyayensu da nufin suje sugai she da iyayen nasu a gida da daddare.

 Dawowarsu ba wuya,  suka tarar da matar aure a dakin daya daga cikin matan nashi a tube tsirara, shima mijin nasu haka suntur.

A cigana da bayanin dai, anan dai sukai ma kwartuwan matan duka,  suka yayyaga mata kayan da tazo dashi, kana suka barta tsirara anan  dai makofta suka tai maka mata da kayan sawa don ta sakaye jikinta. 

Bayan da aka duna fuskae matar, aka gano cewa, Ashe matar abokin shi  kwarton na tane.

Alokacin da Wakilin Jaridar ALFIJIR HAUSA Malam Muhammad Inuwa Zariya, ya zanta da daya daga cikin matan nashi ta shai da Masa cewa, a lokacin da mijin nasu yace su shirya su tafi su je gaishe da iyayen nasu sunyi mamaki matuka sabo da basu tan bayeshi ba yace su tafi Kuma baya barinsu fita anguwa gaba daya biyun sai dai daya ta fita Ashe da makircin daya kulla ne shiyasa ya barsu sufita tare. 

Sai dai shi mijin yace tsaustayi ne yana rokon afuwan abokin nashi daya yafe mashi, wannan mummnuar lamari ya faru ne a maraban jos Kaduna.

0 Response to "An kama wani mutum da matar abokinsa suna tafka lalata a marabar Jos Kaduna"

Post a Comment