--
Wani Matashi yasha fiya-fiya ya mutu, saboda mahaifinsa yaki yi Masa aure a jihar Katsina

Wani Matashi yasha fiya-fiya ya mutu, saboda mahaifinsa yaki yi Masa aure a jihar Katsina

 


Rahotannin da ke shigo mana daga jihar Katsina, sun bayyana mana cewa wani Matashi ya sha guba (fiya-fiya) ya mutu sakamakon Mahaifinsa yaki yi Masa aure.

Lamarin ya faru ne a garin Kafur da ke jihar Katsina Arewacin Najeriya.

Matashin mai suna Abdullahi Tasi’u ya rasu ne bayan ya hada kalanzir da Fetur tare da Gubar Fiya-fiya, inda ya rufe daki ya shanye.

‘Yan uwansa sun jiyo kukansa, Suke je domin Kai dauki, saidai a lokacin da suka shiga sun iske ya galabaita, an daukesa zuwa Asibitin Karamar Hukumar Malumfashi, sai dai kafin akai rai ya yi halinsa.

Kafin ya rasu yana matukar son budurwarsa wadda yaso ace ya aureta, sai dai Mahaifinsa ya hana saboda wasu dalilai da ba a sansu ba

0 Response to "Wani Matashi yasha fiya-fiya ya mutu, saboda mahaifinsa yaki yi Masa aure a jihar Katsina"

Post a Comment