--
Jaruma Hafsat Idris ta auri ɗan Janar Abacha a asirce

Jaruma Hafsat Idris ta auri ɗan Janar Abacha a asirce




Rahotannin sirri sun tabbatar da cewa
jarumar Kannywood, Hafsat Ahmad Idris, ta yi aure a asirce jiya Asabar, 26 ga Fabrairu, 2022.

Wata majiya ta kurkusa da jarumar, wadda ake wa laƙabi da Ɓarauniya saboda fim da ta yi mai wannan sunan, ta shaida wa mujallar Fim cewa an ɗaura auren ne da ɗaya daga cikin ‘ya’yan tsohon shugaban ƙasa, marigayi Janar Sani Abacha.

Majiyar ta ce, “Ɗan Abacha wanda aka haifa a Fadar Shugaban Ƙasa” ne ta aura.

Mujallar Fim ba ta gano wanbe ne daga cikin ‘ya’yan Abachan ba – wato tsakanin Abdullahi da ƙanen sa Mustapha.

An ɗaura auren a asirce a Kano, irin yadda wasu ‘yan fim ɗin Hausa su ke yi. Hakan ya sa ba mu gano inda aka ɗaura auren ba da sadakin da aka biya da kuma waliyyan ango da amarya.

Majiyar mu ta ce an tsara cewa babu wata walimar auren da za a yi kuma amarya za ta tare ne ba tare da ɓata lokaci ba.

0 Response to "Jaruma Hafsat Idris ta auri ɗan Janar Abacha a asirce"

Post a Comment