--
An ɗaura auren Aisha Tsamiya jiya juma'a, duk da ta wallafa cewa an canza rana

An ɗaura auren Aisha Tsamiya jiya juma'a, duk da ta wallafa cewa an canza rana
Duk da iƙirarin da ta yi jiya na cewar ba za a ɗaura mata aure a yau ba, sai ga shi an ɗaura auren fitacciyar jaruma A’isha Aliyu (Tsamiya).

Mujallar Fim ta ambato Aisha a jiya ta na faɗin cewa sai a watan Maris ne za a ɗaura auren nata, ba kamar yadda aka nuna a katin gayyata ba.

Sai dai jim kaɗan da wallafa labarin da mu ka yi a jiya, wata majiya ta kurkusa da Aishar ta shaida wa mujallar Fim cewa tabbas za a ɗaura auren a yau Juma’a, 25 ga Fabrairu, 2022 kamar yadda aka tsara da farko.

Majiyar ta ce Aisha ta yi waccan magana ne kawai don ta basar da mutane.

Lallai kuwa hakan ne ya faru, domin kuwa a safiyar yau aka ɗaura auren A’isha Muhammad Ali da angon ta Alhaji Buba Abubakar.

Sai dai akasin yadda aka nuna a katin, an ɗaura auren a Masallacin Malam Aminu Ibrahim Daurawa da ke Kano, wato an canza lokaci da wurin ɗaurin auren da aka saka a kati.

0 Response to "An ɗaura auren Aisha Tsamiya jiya juma'a, duk da ta wallafa cewa an canza rana "

Post a Comment