--
Jirgin Sojojin Najeriya ya yi barin wuta ga kananun yara, ya kashe 7 bisa kuskure

Jirgin Sojojin Najeriya ya yi barin wuta ga kananun yara, ya kashe 7 bisa kuskure
Rahotannin da ke shigo mana yanzu sun nuna cewa Jirgin Sojojin Najeriya sun kashe kananan yara 7 a Jamhuriyar Nijar a kokarinsu na kashe ‘yan ta’adda.

Jirgin saman yakin sojojin ne ya yi barin wuta akan iyakar Najeriya da Nijar amma maimakon kashe ‘yan ta’addar, sai ya kare da kashe yaran wanda ‘yan Nijar dinne.

Lamarin ya faru a kauyen Nachade ranar Juma’a, 18 ga watan Fabrairu. 

Gwamnan Maradi wanda kauyen ke karkashin ikonsa, Chaibou Aboubacar ya tabbatar da faruwar lamarin.

Gwamnan yace yara 12 ne lamarin ya taba inda 7 suka mutu yayin da sauran ke karbarwar kukalawa a hannun Likitoci.  

Gwamnan yace yayi imanin jirgin na neman ‘yan Bindiga ne yayin da ya kuskure.

Saidai zuwa yanzu hukumomin Najeriya basu ce komai ba kan lamarin

0 Response to "Jirgin Sojojin Najeriya ya yi barin wuta ga kananun yara, ya kashe 7 bisa kuskure"

Post a Comment