Yanzu-Yanzu: Kasa ta rufta da mutane dayawa masu hakar zinari a Nijar
Rahotannin da ke shigo mana yanzu haka sun tabbatar mana da cewa kasa ta rufta da mutane masu hakar Zinare marasa adadi a jihar Maradi da ke Jamhoriyar Nijar.
Yanzu haka da ranar nan ana can ana aikin tono gawarwakin mutanen da kasa ta rufta da su a jihar Maradi ta Nijar da ke aikin hakar Zinare.
Kawo yanzu mun samu labari cewa akwai 'yan Najeriya su 6 daga karamar hukumar Gudu ta jihar Sokoto a cikin wadanda lamarin ya rutsa da su.
Wannan dai shine karo na biyu da kasa take ruftawa da masu aikin hakar zinare a jihar ta Maradi.
Ko a kwanan baya sama da mutun 100 ne su ka rasa rayukkan su a wajen wannan aiki
0 Response to "Yanzu-Yanzu: Kasa ta rufta da mutane dayawa masu hakar zinari a Nijar"
Post a Comment