--
Matashi ya sha guba sakamakon budurwarsa ta yaudareshi a jihar Kano

Matashi ya sha guba sakamakon budurwarsa ta yaudareshi a jihar Kano

 


Rahotannin da ke shigo mana daga jihar Kano da ke Arewacin Najeriya, sun bayyana mana cewa wani matashi mai suna Tijjani Abubakar ɗan asalin unguwar Gama PRP da ke yankin karamar hukumar Nassarawa, ya yi yinkurin kashe kan sa sakamakon cin amanar sa da budurwarsa tayi masa a makon nan.

Lamarin ya faru ne da yammacin yau Talata 15 ga watan Fabrariru na Shekarar 2022 kamar yadda Gidan Rediyon Aminci ya ruwaito.

Wakilin mu Ibrahim Aminu Rimin Kebe ya rawaito matashin ɗan kasuwa sayar da wayar hannu ta Farm Centre yayi wannan yunƙurin ne bayan budurwar da ya shirya angoncewa da ita tace a kai kasuwa, domin ta samu wanda ya fishi iya tattali da soyayya, baya ga maƙudan kudade da yake kashe mata.

Gidan Rediyon ya bayyana cewa za a iya samuj cikyakkyan labarin ta cikin shirin idon mikiya da misalin ƙarfe 10 na dare.

0 Response to "Matashi ya sha guba sakamakon budurwarsa ta yaudareshi a jihar Kano"

Post a Comment