--
Matashi ya cinye waya kirar iPhone 11 tare da dubu 20 bayan sun yi gasa akan wasan PSG

Matashi ya cinye waya kirar iPhone 11 tare da dubu 20 bayan sun yi gasa akan wasan PSG

Wasu matasa gudana biyu sun sanya gasa akan wasan da aka buga tsakanin Kungiyar Kwallon kafa ta PSG da Kuma Kungiyar Real Madrid, Wanda aka yi a ranar Talata.





Matashin mai suna Musa Ramos ya cinye waya kirar IPhone II bayan da tawagar wasan kwallon kafa ta PSG ta ci Madrid daya mai ban haushi a kakar wasan kofin Zakarun Turai ta 2022.

Wannan ya faru ne biyo bayan kulla yarjejeniyarsa da Kaleepha AK 2Pac kan idan PSG ta yi nasara akan Madrid din zai bayar da wayar tasa ga Musa tare da kudi Naira 20,000.

Rahotanni sun nuna cewa shi kuma Musa zai bayar da zunzurutun kudi har Naira dubu dari idan aka samu akasin haka. Me zaku ce?

0 Response to "Matashi ya cinye waya kirar iPhone 11 tare da dubu 20 bayan sun yi gasa akan wasan PSG"

Post a Comment