--
Matsalar Tsaro: Wazirin Katsina ya Ajiye Sarautarsa

Matsalar Tsaro: Wazirin Katsina ya Ajiye Sarautarsa



Wazirin Katsina na biyar a gidan Sarautar Sullubawa, Alhaji Sani Abubakar Lugga, ya ajiye rawaninsa a yau Alhamis 24/2/2022, kamar yadda jaridun Katsina City News suka tabbatar.


Matsalar ajiye sarautar tasa, ta biyo bayan wani jawabi da Wazirin ya gabatar a Ilorin Jihar Kwara a kan matsalar tsaro da kasar nan ke ciki baki daya.


A taron, wajen tambaya da amsa a kan halin tsaro da Katsina ke ciki, Alhaji Sani Lugga, ya ba da bayanin kusan duk abin da manyan Katsina kan furta.


Wannan jawabin nasa, wanda wasu jaridun kasar nan suka dauka a ranar Litinin 21/2/2022, ya harzuka masarautar Katsina, inda ta rubuta masa takardar tuhuma don neman ba da bayani a kan wa ya ce ya je ya yi maganar matsalar tsaron Katsina a Ilori?


A bayanin nasa da ya rubuta, Alhaji Sani Lugga ya ba da hujjojinsa na cewa akwai matsalar tsaro a Katsina har ta shafi Kananan Hukumomi takwas da hujjarsa ta cewa an rufe makarantu, wasu Hakimai na gudun hijira.


A ranar Alhamis Wazirin na Katsina ya ba da amsa cikakkiya mai shafuka hudu da kwararran hujjoji har da maganganun Gwamnan Katsina, Sarkin Katsina da Sakataren gwamnatin Katsina.


A kuma ranar ya aika wa Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman takardarsa ta ajiye sarautarsa.


A wasikar da ya rubuta mai shafuka biyu, ya kawo tarihin sarautar gidansu ta Kanem Bakashe da ke kasar Nijar, wadda ta samo asali tun 1579.


Kazalika ya kawo tarihin sarautar Waziri a gidansu, wadda ta fara tun 1906. Ya kuma ba da bayanin yadda aka nada shi Wazirin Katsina a 2002, wanda ya ce a yau 24/2/2022 ya ajiye.


Sannan ya yi godiya ga Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir, tare da neman gafararsa in har ya bata masa rai.


Jaridun Katsina City News sun ga duk wasikun guda uku, ta farko takardar tuhuma da aka aika wa Wazirin na Katsina a kan maganar da ya yi a Ilorin a kan matsalar tsaro a Katsina da amsar da ya ba masarautar Katsina da kuma wasikar da ya rubuta wa Sarkin Katsina ta ajiye sarautarsa.


An haifi Wazirin Katsina ne a shekarar 1949, yana da takardar Dakta har guda biyu a kan rikici da warware matsala. Yanzu haka Farfesa ne a wannan fannin. Shi ne jigon kafa Jami’ar Musulunci da ke Katsina, kuma ya zama sila na kafa Gidauniyoyin cigaba a Katsina. Kamar Gidauniyar Jihar Katsina da kuma ta Ilmi ta Jihar Katsina.


Alhaji Sani Abubakar Lugga yana da tarihin ajiye mukami in ya ji bai natsu ba. Ya taba ajiye Kwamishinan Ayyuka a zamanin mulkin soja, lokacin da ya ga Gwamnan soja na lokacin yana son ya tilasta masu su yi ba daidai ba. Ya kuma taba ajiye mukaminsa na Jami’ar Musulunci da ya ji ana gunaguni. Yanzu kuma ya ajiye sarautarsa ta Wazirin Katsina.

Daga Dajuma Katsina

nKatsina City News


0 Response to "Matsalar Tsaro: Wazirin Katsina ya Ajiye Sarautarsa"

Post a Comment