--
Abin Tausayi:- Yanzu Wannan Rashin Imanin dame Yayi Kama__Kalli Wani Matashi Yayiwa Tsohuwa Dukan Tsiya

Abin Tausayi:- Yanzu Wannan Rashin Imanin dame Yayi Kama__Kalli Wani Matashi Yayiwa Tsohuwa Dukan Tsiya


 Kotu ta aike da matashi zuwa gidan yari bisa zargin dukan matar aure mai shekara 55


Babbar Kotun Shari’ar Musulunci mai lamba 1 da ke zamanta a kofar kudu,  karkashin jagorancin  Malam Ibrahim Sarki Yola, ta aike da wani matashi mai suna Ghazali Abdullahi Goron Dutse bisa zargin sa da dukan wata matar aure mai suna Halima Abdulhamid, mai kimanin shekaru 55 da haihuwa.


Lamarin ya faru ne  bayan wata hatsaniya da ta shiga tsakanin su a unguwar Kuntau da ke yankin Ƙaramar Hukumar Gwale ta Jihar Kano lokacin da Ghazali, wanda a ke wa lakabi da Ghaza, ya sayi sabuwar mota.


Ya na cikin nuna wa ƴan uwa da abokan motar ne kuma ya na ta danna ƙararrawar motar har ya damu Halima, wacce ta yi masa magana, sai kuma rikici ya shiga tsakani, har ya kai ga ya mata duka nan take.


Daga bisani ne sai ta kai kara caji-ofis domin a bi mata hakkinta.


Sai Kuma bayan ɗan sanda mai gabatar da ƙara, Sifeto Suleman ya gama karanta wa wanda a ke ƙara kunshin tuhume-tuhuman da ake yi masa, sai ya musanta wasu daga ciki, amma kuma ya amsa cewa ya ce mata mutuniyar banza da kuma dukan ta.


Bayan jin ko wane bangare, alkali Sarki Yola ya yi umarni ga jami’an gidan yari da su tafi da shi su ajiye shi har zuwa ranar 16 ga watan Mayu domin ci gaba da sauraron ƙarar.


Cikin kwalla, Hajiya Halima ta bayyana wa manema labarai cewar ko shakka Ghazali ya ci zarafin ta a baynar jama’a, inda ta kuma nuna farin cikin yadda kotun ta fara nema mata hakkin ta.


Ta kuma yi kira ga mahukuntan da su shigo cikin wannan alamarin domin ganin an kwatar mata hakkin nata na cin zarafi ta hanyar duka da ake zargin ya yi mata.

0 Response to "Abin Tausayi:- Yanzu Wannan Rashin Imanin dame Yayi Kama__Kalli Wani Matashi Yayiwa Tsohuwa Dukan Tsiya"

Post a Comment