--
Mata sun fara yiwa Sheikh Daurawa wankin babban bargo, bisa bidiyon da ya saki akan gabansu

Mata sun fara yiwa Sheikh Daurawa wankin babban bargo, bisa bidiyon da ya saki akan gabansu
Mata sun fara yi wa Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa wankin babban bargo kan wani Bidiyo inda yake kiran al'aurar su (Farjin su) abu mafi muni da kazanta. 

Idan ba a manta ba da a wannan Makon ne want bidiyo na Fitaccen Malamin Addinin Musulunci, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi, Inda ya ayyana farjin Mata a matsayin waje mai kazanta Kuma mafi nunin waje abun kyama.


Wannan yasa wasu matan suka fara yi Masa martani da Allah wadai bisa wannan kalamai nasa, inda suka daura a shafukan sadarwa.


A cikin bidiyon matar ta ce "Wai har na ga wani ya yi comment cewa har ya ji ya tsani mata, ya ma yanke shawarar bazai yi aure".


"Yanzu dan Allah fisabilillahi ka kyauta mana mu mata ka kira al'aurar mu abu mafi muni?"

0 Response to "Mata sun fara yiwa Sheikh Daurawa wankin babban bargo, bisa bidiyon da ya saki akan gabansu"

Post a Comment