--
Tirkashi: Matashi Yayi wanka da Kwata saboda Kaunar Banzema Duniya Ina zaki damu

Tirkashi: Matashi Yayi wanka da Kwata saboda Kaunar Banzema Duniya Ina zaki damu


 Innalillahi wainna ilaihirrajuun 


A jiya wani Matashi Yayi wanka da ruwan kwata saboda kaunar Dan wasan Real Madrid mai Lamba Tara (9) Wato karin Banzema,


Wannan lamari yafaru ne a jiyan bayan Kungiyar kwallon Kafa ta Real Madrid ta doke abokiyar karawar ta PSG dachi 3-1 Wanda Banzema ne yayi nasarar Jeff dukkan kwallayen uku (3) a raga,


Hakika wannan lamari abin takaici ne abin kuma bakin ciki ne, idan mukayi duba na tsanaki munsan cewa sufa wadannan yan kwallo ba kaunar mu sukeyi ba,


Duk da wasu na cewa Banzema Musulmi ne amma hakan bazai zama dalili akan irin wannan shirme da wauta ba, hakika Malaman addini sunada sauran aiki a gaban su tayanda kullum burin su suga mutane musamman matasa Sun zama mutanen kirki,


Amma wannan kudiri nasu yana neman lalacewa idan mukayi duba da yanda matasan ke rayuwa a yanzu,


Muna fatan Allah ya karemu daga fadawa irin wannan Hali na rashin tunani da tare da sauran Al'umma gaba daya Ameen.

0 Response to "Tirkashi: Matashi Yayi wanka da Kwata saboda Kaunar Banzema Duniya Ina zaki damu"

Post a Comment