--
Ƴan Bindiga Sun Sace Uwa Da Yaranta Uku A Jihar Katsina

Ƴan Bindiga Sun Sace Uwa Da Yaranta Uku A Jihar Katsina

 



Rahotanni sun bayyana cewa yan Bindiga Sun Sace Uwa Da Yaranta Uku A Jihar Katsina



A daren jiya ne yan bindiga dauke da bindigogi suka kai a cikin garin Funtua a jihar Katsina inda suka sace matar aure Badiyya Shamsu  Muhammad Kalgo da Ƴayanta ukku dake zaune a rukunin gidajen Jikan Malam dake Jabiri a karamar hukumar Funtua.


Majiyar RARIYA ta shaida mata cewa yan bindiga sun samu nasarar kutsawa gidan Malam Shamsudeen Muhammad Kalgo da Misalin karfe dayan daren jiya Litinin, inda suka tafi da Matarsa Malama Badiyya Shamsu da danta Almustapha Shamsu dan Shekara 12 zuwa 13 da diyarta Zainab yar Shekara tara da diyarta Halima Siyama Shamsu yar Shekara Shidda.


Majiyar ta kara da cewa har zuwa haɗa wannan rahoto waɗannan bayin Allah na hannun yan bindiga kuma tun jiya da suka kira Malam Shamsu da daren ba su kara tuntubar su ba.


Allah Ya Bayyanar Da Su Cikin Aminci!

0 Response to "Ƴan Bindiga Sun Sace Uwa Da Yaranta Uku A Jihar Katsina"

Post a Comment