An dakatar da Sheikh Nuru Khalid daga limanci saboda ya caccaki Gwamnatin Buhari Kan matsalar tsaro
Kwamitin kula da masallacin rukunin gidajen ƴan majalisu da ke unguwar Apo a Abuja, ya dakatar da babban limamin Masallacin Shiekh Nuru Khalid kan hudubarsa ta ranar Juma'a.
Sheikh Nuru Khalid a cikin hudubarsa ta ranar Juma'a 1 ga watan Afrilu, ya caccaki gwamnati kan kasa magance matsalar tsaro da kuma yawaitar kashe-kashe a Najeriya.
A cikin hudubar, malamin ya faɗi matakin da ya kamata talakawa su ɗauka idan har gwamnati ta bari aka ci gaba da kashe su, na kin fitowa zaɓe.
"Sharadin talakan Najeriya ya zama guda ɗaya kawai, ku hana kashe mu, mu fito zabe, ku bari a kashe mu, ba za mu fito zaɓe ba, tun da ku ba abin da kuka sani sai zabe," in ji Sheikh Nuru Khalid a huɗubarsa.
0 Response to " An dakatar da Sheikh Nuru Khalid daga limanci saboda ya caccaki Gwamnatin Buhari Kan matsalar tsaro"
Post a Comment