--
DA DUMI-DUMI:- Yan Kwamitin Masallaci sun dakatad da Sheikh Nuru Khalid daga Limanci a Abuja

DA DUMI-DUMI:- Yan Kwamitin Masallaci sun dakatad da Sheikh Nuru Khalid daga Limanci a Abuja


 Yan Kwamitin Masallaci sun dakatad da Sheikh Nuru Khalid daga Limanci a Abuja

Mambobin Kwamitin jagorancin masallacin rukunin gidajen ƴan majalisu da ke unguwar Apo a birnin tarayya Abuja, sun dakatar da Sheikh Nuru Khalid daga limanci a Masallacin.


Shugaban kwamitin Masallacin Sanata Saidu Muhammed Dansadau a jawabin da ya saki ya bayyana cewa an sallami Malam Nuru Khalid ne bisa hudubar da yayi ranar Juma'a, 2 ga Afrilu, 2022, rahoton BBC Hausa. Mambobin kwamitin sunce hudubar Malam Nuru Khalid na tunzura jama'a.A cewar jawabin: "Ina mai sanar da kai cewa an dakatar da kai daga Limamanci a Masallacin ƴan Majalisar da ke shiyyar Apo Abuja daga yau 2/4/22 har zuwa wani lokaci." "An ɗauki wannan matakin ne saboda hudubar Juma'a ta tunzurawa a ranar 1/4/22 inda ka ba mutane shawarar kada su yi zaɓe a 2023 har sai 'yan siyasa sun amsa wasu tambayoyi."


"Ya kamata a ce ka ba su shawara su fito zaɓe don kawar da waɗanda suka saɓa wa Allah, da masu zaɓe da kuma ƙasa."


Kwamitin ya ce hudubar Sheikh Nuru Khalid ta saɓa wa addinin Islama.Me Sheikh Nura Khalid ya fadi a hudubar? A cikin hudubar, malamin ya faɗi matakin da ya kamata talakawa su ɗauka idan har gwamnati ta bari aka ci gaba da kashe su, na kin fitowa zaɓe.


"Sharadin talakan Najeriya ya zama guda ɗaya kawai, ku hana kashe mu, mu fito zabe, ku bari a kashe mu, ba za mu fito zaɓe ba, tun da ku ba abin da kuka sani sai zabe," in ji Sheikh Nuru Khalid a huɗubarsa.

0 Response to "DA DUMI-DUMI:- Yan Kwamitin Masallaci sun dakatad da Sheikh Nuru Khalid daga Limanci a Abuja"

Post a Comment