--
Sojojin Najeriya sun ceto matar da tayi shekaru 8 wajen yan Boko Haram

Sojojin Najeriya sun ceto matar da tayi shekaru 8 wajen yan Boko Haram

 


 


Dangin Shatu Bamai Sangayama (wacce ke jikin hoton da ake kasa) sun gano ta bayan da Dakarun Sojojin Najeriya suka ceto ta daga maɓoyar yan boko Haram a Bama dake jihar Borno. 


Yan ta'addan sun sace ta tun watan Satumba a shekarar 2014 tare da ya'yan ta 4, mata 3 da namiji ɗaya. 


Hoto na farko an dauke shi ne jiya yayin da dakarun sojin Najeriya suka ceto ta daga hannun yan ta'adda a Bama.

Hoto na 2 an dauke shi ne kafin Shekara ta 2014 da aka sace ta, ragowar hotuna biyu na karshe kuma ƴaƴanta ne.


0 Response to "Sojojin Najeriya sun ceto matar da tayi shekaru 8 wajen yan Boko Haram"

Post a Comment