--
YANZU-YANZU: Malamai 6 sun rasu a kan hanyarsu ta dawowa daga yin da'awa a Kano

YANZU-YANZU: Malamai 6 sun rasu a kan hanyarsu ta dawowa daga yin da'awa a Kano


 YANZU-YANZU: Malamai 6 sun rasu a kan hanyarsu ta dawowa daga yin da'awa a Kano 


Rahotannin da su ke iske mu yanzu-yanzu sun baiyana cewa malamai shida ne su ka rasu a haɗarin mota a kan hanyar su ta dawo wa daga Karamar Hukumar Sumaila, Jihar Kano bayan sun je musuluntar da maguzawa, wato da'awa kenan da harshen larabci.


Wata majiya da ga Imamu Malik Foundation, gidauniyar da a  ƙarƙashin ta ne malaman su ke zuwa da'awar, ta ce dukka malamai, shidan waɗanda kuma su ne jagororin da'awar, sun rasu.


A cewar majiyar, a yau da safe ne dai malaman, har ma da wasu ɗaliban su, su ka tafi Sumaila ɗin domin musuluntar da maguzawa.


Sai dai majiyar ta ce ba su samu labarin cewa ɗaliban sun rasu ko sun ji raunuka ba, amma ta tabbatar da cewa malaman duk sun rasu.


Ta ce Mallam Alƙassim Zakariyya, shine jagoran tafiyar, shima ya rasu.


"Yanzu haka muna can Imamu Malik Foundation a unguwar Dakata, muna jiran sauran ɗalibai su karaso sai mu wuce gidan Sheikh Alƙassim Zakariyya, inda a nan ne za a yi musu jana'izar," in ji majiyar, wacce ta nemi a dakatar sunan ta.


Da mu ka tuntuɓi Kakakin Hukumar Kare Hadarurruka ta Ƙasa, FRSC, a Kano,  Abdullahi Labaran ya ce har yanzu dai basu samu labarin ba amma zai bincika.


Ƙarin bayani na nan tafe...

0 Response to "YANZU-YANZU: Malamai 6 sun rasu a kan hanyarsu ta dawowa daga yin da'awa a Kano "

Post a Comment