--
Muna Yabawa Shugaban Kasa Bisa Bude Rumbunan Abinci Saboda Azumi, Sheikh Bala Lau Read more: https://hausa.legit.ng/news/1465716-muna-yabawa-shugaban-kasa-bisa-bude-rubunan-abinci-saboda-azumi-sheikh-bala-lau/

Muna Yabawa Shugaban Kasa Bisa Bude Rumbunan Abinci Saboda Azumi, Sheikh Bala Lau Read more: https://hausa.legit.ng/news/1465716-muna-yabawa-shugaban-kasa-bisa-bude-rubunan-abinci-saboda-azumi-sheikh-bala-lau/



Kungiyar da'awar addinin Musulunci, Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa Iqamatis Sunnah JIBWIS, ta jinjinawa shugaban kasan bisa umurnin fitar da hatsi daga rimbun abincin gwamnati. Shugaban kungiyar, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya jinjinawa wannan mataki da ya dauka, wanda a cewar sa zai kawo sauki matuka ga al'umma.


Ya bayyana hakan a jawabin da ya saki a shafin JIBWIS na Facebook. Idan ba a manta ba dai, a watan da ta gabata, Sheikh Bala Lau yayi kira na musamman ga shugaban kasa da ya bude rumbunan abinci da asusun gwamnati saboda tallafawa al'umma a cikin watan Ramadaan.


Sheikh Lau yayi wannan kira ne a lokacin da shugaban kasan ya halarci bude babban masallaci da kungiyar IZALA ta gina a Abuja.


Bala Lau yace: "Alhamdulillah, muna jinjina ga shugaban kasa, wannan ba karamin taimakawa talakawa zai yi ba." "Kuma muna kira ga hukumomin da alhakin raba wannan kaya ya shafa su hada kai da shugabannin al'umma da suka fi kusa da su kamar malamai da sarakuna wajen raba wannan tagomashi don ganin cewa wannan tallafi ya isa zuwa ga talakawa."


ya bada umurnin fitar da kayan hatsi ton 40,000 daga rumbun kayan masarufin gwamnati don taimakawa talakawa wajen murnin bikin Easter, azumi da sallah


Ministan noma da raya karkara, Muhammad Mahmoud, ya bayyana hakan yayin hira da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan ganawarsa da shugaban kasa. Kamfanin dillancin labaran Najeriya NAN ya bayyana cewa Mahmoud ya gaba da Buhari ne ranar Talata, 12 ga Afrilu, 2022.


A cewarsa, sakin wadannan kayan hatsi zai rage farashin kayan masarufi a kasuwa. Ya kara da cewa cikin ton 40,000 da za'a saki, za'a baiwa ma'aikatar Hajiya Sadiya Farouq ton 12,000 don rabawa yan gudun hijra dake fadin tarayya.


Source: Legit.ng

0 Response to "Muna Yabawa Shugaban Kasa Bisa Bude Rumbunan Abinci Saboda Azumi, Sheikh Bala Lau Read more: https://hausa.legit.ng/news/1465716-muna-yabawa-shugaban-kasa-bisa-bude-rubunan-abinci-saboda-azumi-sheikh-bala-lau/"

Post a Comment