--
 A dukkan akidun Musulunci Babu Akidar Dana Tsana A Baya Irin Shi'ah, Da naji Kai Ɗan Shi'a Toh Fa Babu Ni Babu Kai

A dukkan akidun Musulunci Babu Akidar Dana Tsana A Baya Irin Shi'ah, Da naji Kai Ɗan Shi'a Toh Fa Babu Ni Babu Kai


A Akida Babu Akida Dana Tsana A Baya Irin Shi'ah, Da naji Kai Ɗan Shi'a Toh Fa Babu Ni Babu Kai. Daga:Jamila Ibraheem(Home of solace) 

Munada makwabta yan shi'a bana hada harka ta dasu kwata kwata kowa addininsa yake baya  kula wani...

Kumafa sunada kirki sosai fiye da tunanin mutane ,  amma sabida akidar su yasa na tsane su

Sai watarana yarona ya tashi da convulsion idonsa a sama hakoransa nata hadewa gashi babu babansa a gida yayi tafiya ,  waenan makwabtar nawa suka kaimu asibiti karfe biyu na dare , suka tsaya dani har aka gama treatment ,  su suka biya hospital bills gaba daya muka dawo gida ...

Wlh Allah nayi dana sanin rashin kulasu da banayi ...

Tun daga wannan lokacin muke zama lafiya dasu , kowa na yin addininsa bana shiga hurumin tasu akidar , 

suma basu shigan nawa dukda ni ban dau akida ba kawai abunda musulunci ya kawo kuma yake sunna dashi nake amfani ban tsaida akida ba amma bazanyi shi'a ba ...

Don haka yan uwa mu zauna da abokanmu lafiya kowa yayi akidar sa ,  idan munje lahira Allah zai tantance mu da kansa

Bamusan wanda zai mana rana ba karshe sabida akida muzo mu sami matsala..

Kayi musulincin ka da naka akidar kar wani ya sa kayi wani abu wanda musulinci bai yarda dashi ba ,  amma kuma kar hakan ya hanaka abota ko zama lafiya da wanda ba akidarku daya ba 

Da fatan kun wayi gari lafiya

0 Response to " A dukkan akidun Musulunci Babu Akidar Dana Tsana A Baya Irin Shi'ah, Da naji Kai Ɗan Shi'a Toh Fa Babu Ni Babu Kai"

Post a Comment