Ana Yakar Arewa Ta Fuska Uku, Amma Mutanen Yankin Ba Sa Ganewa_ Sheikh Ibraheem El-Zakzaky duba abinda yace
Ana Yakar Arewa Ta Fuska Uku, Amma Mutanen Yankin Ba Sa Ganewa_ Sheikh Zakzaky
Daga: Abdulrashid Kabir Gwanimi
1-Noma. wadda ita ce tushen arzikin mutanen yankin, yanzu ta gagara, an hana manoma aiki an kore su daga garuruwan su, wanda ya zauna za a kashe shi.
2-Kiwo. Makiyaya an kashe ana kwashe dabbobin su.
3-Kasuwanci. Sufurin kayayyaki ya zama hadari, saboda ayyukan 'yan ta'adda a hanyoyi. Sai gobara a kasuwanni wadda ba ta lafiya bace a rasa mai ya haddasa ta. Dan kasuwa idan yabi hanya a sace shi a nemi kudin fansa, sai dai a kwashe jarin sa a fanso shi ya dawo ba abin juyawa.
Su kuma manyan yankin ba wannan ne ya dame su ba, in dai za a ba mutum mukami shi kenan kawai.
0 Response to "Ana Yakar Arewa Ta Fuska Uku, Amma Mutanen Yankin Ba Sa Ganewa_ Sheikh Ibraheem El-Zakzaky duba abinda yace"
Post a Comment