--
EFCC Ta Kama Ahmed Idris, Babban Akanta Na Kasa Saboda Almundanar Nera Biliyan Tamanin N80billion

EFCC Ta Kama Ahmed Idris, Babban Akanta Na Kasa Saboda Almundanar Nera Biliyan Tamanin N80billion


EFCC Arrests  Ahmed Idris,  Accountant General of the Federation for N80billion Fraud.


 Hausa Translation:


EFCC Ta Kama Ahmed Idris, Babban Akanta Na Kasa Saboda Almundanar Nera Biliyan Tamanin


Hukumar EFCC ranar Litinin 16 ga watan Mayu, 2022, ta kama babban akanta na kasa mai ci, Ahmed Idris saboda tuhumar sa da take na karkatarwa da safarar kudin haram kimanin nera biliyan tamanin.


Binciken hukumar EFCC ya gano cewa babban akantan ya yi amfani da ‘yan uwa da abokan arziki da sauran makusanta wajen karkatar da kudin da aikata sauran laifin da ake tuhumar shi da shi.


An yi amfani da kudin wajen saka hannun jari a fannin gidaje a jihar Kano da Abuja.


Hukumar ta kama shine bayan katin gayyata da ta aika masa da ya halarci ofishinta don amsa wasu tambayoyi amma yaki amsakatin gayyatar.


Ku ziyarci sashen intanet na EFCC www.efccnigeria.org don karanta karashen labarin.

0 Response to "EFCC Ta Kama Ahmed Idris, Babban Akanta Na Kasa Saboda Almundanar Nera Biliyan Tamanin N80billion"

Post a Comment