--
Jerin abubuwa masu daraja guda biyar da jihar Kano take dashi ita kadai

Jerin abubuwa masu daraja guda biyar da jihar Kano take dashi ita kadai


YAU SHEKARU 55 DA BAWA KANO JIHA.Daga cikin abubuwan da Allah ta'alah ya yiwa wannan gari na Kano:-(Daraja ta 1)

Fannin Addinin Musulunci ta yi Zarrah

Yadda ta tattara manyan Malamai da Gidajen su, Ɓangaren Tauhidi, Fiqihu, Tafsiri, Liqqa, uwa uba dasa ƙaunar Shugaba ﷺ, Ina tuna Gwarzon Musulunci, Sarkin Yaƙin Shehu Usman Ɗanfodiye Maulana (Dr.) Sheikh Muhammad Nasir Kabara (R.a). Kuma yanzu a Ilimin zamani ma ta yi Zarrah a ɓangare daban daban, ta tara Furofesosi da Daktoci da masu tasowa yanzu, ga tarin Makarantu iri-iri. Haka na:

Jagorancin Qadiriyyah yana Kano.

Jagorancin Tijjaniyyah yana Kano.(Daraja ta 2).

Tayi Zarrah a kasuwanci har ake kiranta da cibiyar kasuwanci ta Najeriya.

Wacce Jiha take da Gidan Marigayi Alh. Alasan Ɗantata.?

Alh. Aliko Ɗan Gwate?

Alh. Abdussamad Ishaq Rabi'u?

Ga manyan Kasuwanni kamar 

1. Abubakar Rimi (Sabon Gari)

2. Kantin Kwari

3. Sheikh Nasir Kabara (kasuwar k/wanbai)

4. Kasuwar Kurmi me daɗaɗɗen Tarihi da sauransu.(Darajah ta 3)

Fannin Sarautah 

Kano ta sha banban da sauran garuruwa wajen samun gwaraza akan Sarauta, da irin yadda Sarautar take da kayan Tarihi masu yawa, tun daga gidajen Sarautar, da kayan Sarautar. Saboda girman Sarautar Kano ba inda ake sawa Ido kamar ta, don aga irin salon da take zuwa da shi.Tun kafin Sarki Kano Dabo, Kano tayi Zarrah har zuwa Marigayi Alh. Ado Bayero, domin ya aje Tarihi, ga Murabus Khalifa. Sunusi Lamiɗo, shi ma yayi nasa ƙoƙarin, yanzu ma da yake Murabus a hakan yafi wasu Sarakunan Sarauta🤣Ga kuma Saraku 5 da ake da su a yanzu

1- Sarkin Kano

2- Sarkin Bichi

3- Sarkin Karaye

4- Sarkin Rano

5- Sarkin Gaya(Darajah ta 4)

Tayi Zarrah a harkar Siyasa tun kafa ƙasar nan ta zama uwar Siyasar Nigeriya, ko Shugaban ƙasa kake nema idan ka rasa kaso mai tsoka a Kano to ka gama faɗuwa. Allah ya rabauta mu da ƴan Siyasa iri-iri kamar su: Marigayi Mal. Aminu Kano, Marigayi Abubakar Rimi, Dr. Rabi'u Musa Kwankwaso, wanda yake fafatawa yanzu haka don neman zama Shugaban kasar Nijeriya 2023. Muna fata Allah ya lamunce,  ga su Dr. Ibrahim Shekarau, Dr. Abdullah Umar Ganduje da sauran su.(Darajah ta 5)

Kaɗan daga kirarin da ake mata:- 

_KANO ta Dabo Cigari

_KANO tumbin giwa ko da me ka zo an fika

_KANON Dabo birni mai mata mai mota.

_KANO tinjimin gari mai Dala da Goron Dutse 

Gari ba Kano ba dajin Allah. 

_KANO garin Ilimi da Malamai

_KANO garin mulki da sarakuna

_KANO garin Arziki da Attajirai

_KANO cibiyar kasuwanciDa sauran abubuwa masu yawa da ban ambata ba. Allah ya ƙara yiwa nannan Jiha tamu ta Kano albarka, ya ƙara bamu lafiya da zaman lafiya a ɗaukacin ƙasar mu Najeriya baki ɗaya,  da sauran ƙasashen Musulmi da ke faɗin duniya Amin.Mhmd Ni'imatullahi Khalil Getso 27/05/2021.

0 Response to "Jerin abubuwa masu daraja guda biyar da jihar Kano take dashi ita kadai"

Post a Comment