--
Wannan labarin na daban ne Mace Da Namiji Masu Hankali ya Zama Dole Su Dubashi Ku Latsa Nan Akwai Darasi

Wannan labarin na daban ne Mace Da Namiji Masu Hankali ya Zama Dole Su Dubashi Ku Latsa Nan Akwai Darasi


Direban Taxi ya ce, na ɗauki wata Dattijuwa da Ƴarta, sai ƴar take cewa, ni fa gaskiya Mama na gaji da wannan mijin nawa, kullum mutum sai Masifa, abu kaɗan ne yake ɓata masa rai....!!!


Dattijuwa ta ce, ƴata shi namiji ana mu'amala da shi ne gwargwadon hankalinsa, dole ki koyi siyasar zamantakewa. 


Ni da Babanki mun fi shekara 40 da aure amma bamu da wata matsala, duk abin da ya ce, zan ce masa "An gama", ki ƙyalle shi ya ji kamar shi ne yake juya al'amuran gidan, wanda a Zahiri kuwa Raƙumi ne da akala.


Ƴata su fa Maza kamar Shashashai suke kalma ɗaya ce ta ke tafiyar da fushinsu....!!!!


Ɗan Taxi ya ce, sai na fusata, na tsaya a gefen Titi ina kallon dattijuwar nan ta gefen mudubi, sai ɓacin rai ne yake damuna, ta ya ya za a ce duk maza kamar "Shashashai" suke...


Dattijuwar nan sai ta kalli Ƴarta ta ce, sai dai fa wannan Ɗan Taxi ɗin, shi kam da alama daban ne a cikin maza, na ga ɗan albarka ne.


Ɗan Taxi sai ya yi murmushi, ya tuƙa mota suka cigaba da tafiya, sai murmushi yake yi.


Ta raɗawa ƴarta ta ce, kin ga yadda suke ko, na gaya miki kamar "Shashashai" suke, kalma ɗaya tak zaki faɗa su yi shiru, kuma su daina tafasa....!!!!!

0 Response to "Wannan labarin na daban ne Mace Da Namiji Masu Hankali ya Zama Dole Su Dubashi Ku Latsa Nan Akwai Darasi"

Post a Comment