--
Zaben 2023: Anya APC za ta kai labari kuwa? Atiku fa ya dagula musu lissafi,

Zaben 2023: Anya APC za ta kai labari kuwa? Atiku fa ya dagula musu lissafi,


Zaben 2023: Anya APC za ta kai labari kuwa? Atiku fa ya dagula musu lissafi, 


Daga: Ahmed Tijjani Ramalan


IYA RUWA FIDDA KAI: 

APC ta ce ba za a yi maslaha ba a zaben fidda dan takarar shugaban kasa


Tsakani da Allah Jam’iyyar APC ta shiga cikin ruɗani da jagwalgwalo ta n bayan nasarar da Atiku Abubakar yayi a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar PDP.


Abin ya kaiga shi kansa shugaban kasa Muhammadu Buhari na shirin yi wa jam’iyyar karfakarfa wajen ayyana wanda yake so kuma tilasta gwamnoni da ƴan jam’iyyar su bi ko suna so ko basu so. Abinda ya ke neman ya kifar da jam’iyyar shine wanda zata zaba ya cira mata tuta a zaɓen shugaban kasa mai zuwa. Wanda zai iya gobzawa da Atiku ya kuma iya kada shi.


Akwai daɗaɗɗiyar alkawari tsakanin jam’iyyar da ƴan takara daga kudancin Najeriya, musamman tsohon gwamnan jihar Legas Bola Tinubu wanda da shi ne aka kafa jam’iyyar APC a 2014. Saidai kuma ruwa na neman ya cinye ɗan kada domin ga dukkan alamu dai wannan magana bata yanzu, wani ne daban ake ganin shi kansa shugaba Buhari ya ke so ba Tinubu ba.


Idan har haka ya auku, toh lallai akwai rigina a gaba domin Tinubu ya ce ba zai ɗaga wa kowa ƙafa aba neman wannan kujera bakin rai bakin fama.


Sama da ƴan takara 20 ne suka sayi fom ɗin rakarar shugaban kasa a jam’iyyar APC, kuma dukkan su sun lashi takobin za a fafata da su ba za su janye ba. Wasu ƴaƴan Jam’iyyar, ciki harda tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Uzor Kalu ya gargaɗi jam’iyyar cewa kada su kuskura baiwa ɗan kudu takara domin ba zai yi nasara a zaɓe ba. Ya gargaɗi APC su baiwa ɗan yankin Arewa ne wanda zai fafata da Atiku, ya kum kada shi.


Amma kuma a jerin waɗanda suka sayi fom ɗin APC ɗin daga Arewacin Kasara nan babu wanda ake ganin zai ya kai Atiku kasa a zaɓen 2023. Tinubun ne dai zai iya fafatawa da Atiku ayi kare jini biri jini a zaɓen shugaban kasa.


Amma kuma wannan dama na yin takarar na neman ta yi masa nisa ga dukkan alamu. Ifan ko haka ya auku, akwai yiwuwar APC din da kanta zata ruguje, za asamu ruɗani da rarrabuwar kawuna wand zai sa jam’iyyar PDP ta yi nasara a kasa da wasu jihohin APC ɗin.


Yanzu dai dabara ya rage ga mai shiga rijiya, ko APC ta na tsu na yi abinda ya dace, wato ayi zaɓe, gar da gar, wanda ya ci a bashi, ko kuma ta ɓare kowa ya rasa.

0 Response to "Zaben 2023: Anya APC za ta kai labari kuwa? Atiku fa ya dagula musu lissafi, "

Post a Comment