--
Ina Matan Hausawa? Wasu Mata Biyu Sun Gwangwaje Mazajensu da Motocin Miliyan 87

Ina Matan Hausawa? Wasu Mata Biyu Sun Gwangwaje Mazajensu da Motocin Miliyan 87


Ina Matan Hausawa? Wasu Mata Biyu Sun Gwangwaje Mazajensu da Motocin Miliyan 87


Kafin yanzu, maza ne aka fi sani da da dabi’ar ba wa matansu, ‘yan matansu da wadanda zasu aura kyautar motoci a matsayin ba-zata kafin wasu mata su canza salon kidan. Wasu mata da suka bawa mazajensu da suke matukar kauna kyautar sabbin motoci.


Wata mata ‘yar Najeriya ta gwangwaje masoyinta da sabuwar mota a ranar zagayowar aurensu a watan Satumban 2021, matar ‘yar Najeriya ta tada kura a shafukan sada zumuntar zamani bayan tayi wa mijinta kyautar ba-zata a sabuwar mota.


Matar mai suna Adeyemi Holubunmy Crown ta mallaka wa mijinta sabuwar motar ne a ranar zagayowar shekarar aurensu na bakwai.


Yayin da ta damka masa mukullin motar, matar ta rubuta a shafinta na Facebook:


“Wannan kadan ne daga cikin irin kaunar da nake maka. Ina matukar kaunarka kuna babu abun da zai canza hakan. Crown Kay Amos kafi kowa.”

An ga yadda mijinta Crown Kay Amos ke murmushi a hotunan yayin da ya amsa kyautar motar daga rabin ransa.


Haka kuma,


Wata mata mai juna biyu ta gwangwaje mijinta da motar N87 miliyan cikin watan Maris, matar mai shekaru 19 ta matukar ba wa masu amfani da yanar gizo mamaki da kyautar da ta wa mijinta.


Matar mai suna Anes Ayuni Osmanis ta mallaka masa sabuwar mota kirar Lamborghini Huracan Evo wacce ta kai kimar N87 miliyan gami da wallafa bidiyon lokacin da ta kai shi wajen siyar da motocin inda aka bude sabuwar motar.


A al’adarta, ana sa ran mijin ne zai kula da jinjirin idan an haifesa har sai ta dawo daga gida wanka.


Kyautar motar da matar ‘yar Malaysia tayi hanya ce na saka wa masoyinta rainon jinjirin da zai yi wanda ya zama masa wajibi.


Mijinta ya yi matukar farinciki a bidiyon.

0 Response to "Ina Matan Hausawa? Wasu Mata Biyu Sun Gwangwaje Mazajensu da Motocin Miliyan 87"

Post a Comment