--
Muhimman Hanyoyi Da Zakubi Domin Samun Rancen NIRSAL CREDIT RISK GUARANTEE

Muhimman Hanyoyi Da Zakubi Domin Samun Rancen NIRSAL CREDIT RISK GUARANTEE


Shugaban Hukumar dake bayar da lamuni kan harkar noma ta babban bankin Najeriya NIRSAL Aliyu Abbati Abdulhameed ya ce a halin yanzu hukumar ta fara bayar da lamuni ga manoma da kuma masu yin dukkan ayyuka da suka shafi noma domin samar da isashshen abinci a Najeriya.


Wannan sanarwar na zuwa ne a yayin da kasashen nahiyar Afirka da dama ke lalubo hanyoyin bunkasa harkar noma domin yalwar abinci a kasashensu.


Aliyu ya ce idan a kan harkar da ta shafi noma ne, hukumar za ta iya bayar da lamuni ga mutum daga Naira daya har Naira biliyan daya.


An kafa hukumar NIRSAL ce a shekara ta 2011 domin bayar da lamuni ga duk mai hada-hada da kuma zuba jari a cikin harkar noma.


"Abin da muke nufi da noma shi ne ba wai kawai shiga gona ko kiwon kaji ko kiwon dabbobi kadai ba, duk harkar da ta shafi noma da kiwo daga sarrafawa har zuwa sufuri da kuma sayarwa za mu ba su lamunin samun bashi a wajen bankuna ko kuma masu saka jari daga Naira daya har Naira Biliyan daya" in ji Aliyu Abdulhameed.


Shugaban hukumar ta NIRSAL ya kara da cewa idan banki ko mai saka jari ya saka kudinsa, idan aka samu asara hukumar NIRSAL za ta biya.


Matakan samun lamunin NIRSAL.


1. A rubuta wa daya daga cikin bankunan Najeriya takardar neman rance, sannan a nemi sahalewar hukumar NIRSAL domin lamuni.


2. Banki zai dubi takardar neman rancen, sannan ya aika wa hukumar NIRSAL dukkan takardu da ake bukata a madadin mai neman rance.


3. Hukumar NIRSAL za ta dubi takardun da banki ya mika mata sannan ta tabbatar da sahihancinsu da kuma cikarsu cif-cif.


4. Idan banki da kuma hukumar NIRSAL suka tabbatar da duk takardu sun cika, sai su ziyarci gona ko wurin kasuwancin mai neman lamunin.


5. Idan har hukumar da kuma banki suka aminta da ingancin harkar noma ko kiwo ko kuma kasuwancin da mutum ya shirya yi, sai NIRSAL ta bayar da lamuni ga mai neman rancen ta hannun banki.


6. Daga nan sai banki ya bai wa mutum kudin da ya nema rance domin fara sana'arsa, sannan ita kuma hukumar NIRSAL ta fara sanya ido kan yadda sana'ar ke gudana.


Rahoton: BBC HAUSA

0 Response to "Muhimman Hanyoyi Da Zakubi Domin Samun Rancen NIRSAL CREDIT RISK GUARANTEE"

Post a Comment