Abubuwa 2 wadanda maza ke yinsu da mata suka tsana
Maza suna yawan yin abubuwan da ke ɓatawa matan su rai. Maza, wannan darasin naku ne! Ku yi kokari ku gano wasu abubuwan da kuke aikatawa waɗanda matan ku basa so amma kuma su ba za su iya bayyana muku ba.
Ga wasu muhimman abubuwa biyu da ya kamata kusani da maza suke yi da yake ɓatawa mata rai.
1. Mazan Da Kwata-Kwata Basa Tambayar Mace Ko Nuna Damuwa Akan Halin Da Suke Ciki
Kai ba Chris Evans bane kuma ni ba Jimmy Fallon bane. Ina tsammanin hakan a bayyane yake, daidai ne? Don haka me yasa kuke nuna rashin damuwarku akan masoyan ku. Mata sun tsani namijin da ba ya tambayar halin da suke ciki.
Duk mace tana son kulawa daga wajen namiji wanda zai dinga nuna damuwarsa akan ta tare da nuna damuwarsa akan yanayin da ta ke ciki na rashin jindadi.
Maza da dama ba su damu da su ji damuwar matan da suke zaune tare dasu ba. Hakan yasa matan suke kara shiga wani yanayi na rashin jindadi a rayuwarsu.
2. Rashin Nuna Soyayya
Duk mace tana so da burin ganin namijin da ta ke so ya damu da ita, sai dai maza da dama idan sun fuskanci mace na kaunar su sai su dinga yi musu wulakanci da girman kai, maimakon shima ya nuna mata kauna sosai amma sai ya nuna bai damu da ita ba .
Mace tana son kulawa sosai daga wajen namijin da ta ke so domin hakan yana kara saka mata nishadi da kwanciyar hankali a rayuwar ta. Amma indai ba za ta samu kulawa ba duk za ka samu ba ta da kuzari da annashuwa.
Da fatan maza za su Kula sosai wajen nuna soyayya ga matan su. Domin hakan zai kara kwantar mata da hankali da jindadin rayuwar ta.
0 Response to "Abubuwa 2 wadanda maza ke yinsu da mata suka tsana"
Post a Comment