Ɗaliban Education Masu Karatun Digiri Za'a Basu N75,000 (Degree), suma kuma Ɗalibai Maau NCE N50,000 duk semester
Ɗaliban Education Masu Karatun Digiri Za'a Basu N75,000 (Degree), suma kuma Ɗalibai Maau NCE N50,000 duk semester
Kwanakin baya gwamnatin Nigeriya ta karɓi bayanan dukkanin ɗaliban da suke karantar Education a jami'o'i da NCE kan wani ƙudurun su da bai kammala inganta ba a lokacin. Ya zuwa yanzu bayan karɓar bayanan dukkanin wanda suke karantar Education a Nijeriya, sun alƙawarta, a ƙoƙarin su na inganta harkar ilimi zasu na bawa kowanne ɗalibi 75k (Degree) da 50k (NCE) duk semester har su kammala karatun su.
Amma, dole sai mutum ya cike ta link ɗin da suka bayar, idan ka cike shikkenan idan baka cike ba ka rasa, banda kai za'a na samun wannan tallafi. Saboda ƙin cikewar na nuna rashin sha'awarka akan tsarin.
Wannan babu wata test da za'a yi, babu ƙa'idar shekara, babu wasu dokoki masu tsauri, kawai ana bukatar ka kasance mai karantar Education ne kawai, kuma a yanzu; ba part time ba, ba kuma ka kammala karatun ka ba.
Note:
•Idan dai kai ɗalibin Education ne tuni bayanan ka yana hannun su.
•Idan baka cike ba kamar ka nuna baka sha'awa ne.
•Idan ka cike, a cire maka slip ɗin ya kasance yana hannun ka, sai ka haɗa copy ɗin ID card ɗin ka, da admission letter ka sai ka jira su.
•Kada ka kuskura ka cike sau biyu domin hakan zai sa a cire sunan ka daga tsarin automatically. Saboda haka a kiyaye, idan baza ka iya ba kaje cafe a cike ma.
•Idan ka kammala karatu ka cike kana bawa kanka wahala ne.
•Duk wanda Federal government ta taɓa bashi scholarship banda shi. Amma, banda wanda yake nema, domin bai samu ba tukuna.
Ga link:
0 Response to "Ɗaliban Education Masu Karatun Digiri Za'a Basu N75,000 (Degree), suma kuma Ɗalibai Maau NCE N50,000 duk semester"
Post a Comment