Ba da yawuna Lauyana ya nemi a yi min sassauci ba - Sheikh Abduljabbar Kabara
Ba da yawuna Lauyana ya nemi a yi min sassauci ba - Sheikh Abduljabbar Kabara
Kai tsaye daga Kotun Ƙofar Kudu.
Kotu ta ce, ta samu Abduljabbar Kabara da laifin yiwa ma'aiki (s a.w) kage da cin mutumcin ma aiki da cewar yayi fyade ,
An same shi da laifi karkashin sashe na 382 (B)
Lauyan da ke kare shi Barrister Aminu Abubakar yace ayi masa sassauci saboda kuskuren fahimta ce tasa Malam Abduljabbar ya aikata wannan laifi.
Amma nan take malamin ya miƙe ya ce shi dai ba da yawunsa ba, Lauyana yake magana.
Malamin ya ce, baya neman sassauci, kuma yana neman a gaggauta yi masa hukunci domin zai yi mutuwa ta girma.
Ku ci gaba da bibiya, zamu ci gaba da kawo muku yadda take kasancewa.
0 Response to "Ba da yawuna Lauyana ya nemi a yi min sassauci ba - Sheikh Abduljabbar Kabara"
Post a Comment