--
Babu Gudu Ba Ja Da Baya Kan Sabon Tsarin Takaita Cire Kudi - Emefiele

Babu Gudu Ba Ja Da Baya Kan Sabon Tsarin Takaita Cire Kudi - Emefiele




Babu Gudu Ba Ja Da Baya Kan Sabon Tsarin Takaita Cire Kudi - Emefiele

 


Babban bankin Najeriya, ya ce babu fashi kan sabon tsarinsa na takaitawa ɗaidaikun mutane cire kudi daga bankuna bayan kiraye-kiraye daga ko'ina a Najeriya cewar ya sake duba batun.


Gwamnan babban bankin, Godwin Emefiele ne ya bayyanawa manema labarai hakan bayan ganawa da shugaba Muhammadu Buhari.


Ya ce batun da bankin zai sake dubawa shine adadin kudin da za a iya cirewa ba wai ya canja tsarin ba, inda ya ce sabon tsarin na nan daram.


Gwamnan babban bankin na magana ne bayan da majalisar wakilai ta nemi da a soke tsarin da kuma gayyatarsa zuwa gabanta domin ya yi mata bayani.


“Ina sane da batun jin karin bayani da 'yan majalisa suka nema. Amma ina ganin abu mafi muhimmanci shi ne cewa tsarin ya faro ne tun a shekara ta 2012,'' in ji Emefiele.


“Sai dai kusan sau uku zuwa hudu muna soke tsarin saboda muna ganin ya kamata mu yi kyakkyawan shiri da sake gyara tsarin biyan kudi a Najeriya.


''Tsakanin 2012 zuwa 2022, kusan shekara goma kenan, muna da yakinin cewa an samar da cibiyoyi na taimakawa mutane da dama yin hada-hadar kudaɗe a fadin kasa.


Emefiele ya ce akwai tsari da za a yi wa al'ummomi a karkara don tabbatar da cewa sabbin tsare-tsare ba su yi mummunan tasiri a kansu ba.


A ranar Talata ne, CBN ya taƙaita yawan kuɗade laƙadan da ƴan ƙasar za su iya cirewa daga asusun ajiyarsu na banki, inda yawan kuɗin da mutum ɗaya zai iya fitarwa a banki a sati shi ne naira 100,000 yayin da kamfani zai cire naira 500,000 ne kawai a sati.

0 Response to "Babu Gudu Ba Ja Da Baya Kan Sabon Tsarin Takaita Cire Kudi - Emefiele"

Post a Comment