--
'Da kuɗin tallar lemu na tura ƴata makaranta har ta zama lauya'

'Da kuɗin tallar lemu na tura ƴata makaranta har ta zama lauya'

 


Ta ce "na sha wahalar rainon ta tun tana ƙarama, na sayar da lemu, babu abin da ban yi ba domin ganin ta je makaranta har ta zama lauya, yanzu ne ya kamata na ci moriyar wahalar da na sha..."



Mahaifiyar lauyar da ƴan sanda suka kashe a Legas, Bolanle Raheem na cikin matsanancin alhinin kisan ɗiyarta.

Ga cikakken video 

👇👇👇👇👇

https://youtu.be/y8wZkuPKWcs



Ta kuma yi bayanai da dama a lokacin da kwamishinan ƴan sanda na jihar, Abiodun Alabi ya kai mata ziyarar jaje a gidanta, ranar Talata.


Ta ce "kwamishina, wannan ba abu ne mai sauƙi ba, yarinya ce da na sha wahalar renon ta tun tana ƙarama, na sayar da lemu, babu wani abu da ban yi ba domin ganin ta je makaranta har ta zama lauya, yanzu ne ya kamata na ci moriyar wahalar da na sha, Allah ka ƙwato min hakkina."


Ta faɗi hakan ne tana cikin damuwa yayin da mutane ke rirriƙe ta.

0 Response to "'Da kuɗin tallar lemu na tura ƴata makaranta har ta zama lauya'"

Post a Comment