--
Musbahu M Ahmad Yayiwa Sheikh Idris Abdulaziz Bauchi Zagin Kare dangi Akan Maganar da Yayi Na cewa duk Yan Fim Jahilaine

Musbahu M Ahmad Yayiwa Sheikh Idris Abdulaziz Bauchi Zagin Kare dangi Akan Maganar da Yayi Na cewa duk Yan Fim Jahilaine




Musbahu M Ahmad Yayiwa Sheikh Idris Abdulaziz Bauchi Zagin Kare dangi Akan Maganar da Yayi Na cewa duk Yan Fim Jahilaine



 Tsohon Jarumi a Masana’antar Kannywood Musbahu M Ahmad Yayiwa Fitaccen Malamin Addinin Musulunci nan watau Sheikh Idris Abdulaziz Bauchi Wankin babban bargo Akan Maganar yayi na cewa a kaf yan fim babu me addini duk Jahilaine.


Fitaccen malamin wanda ya taba cewa gara kashi da Maulidi Yanzu kuma ya kara kawo wata maganar akan jaruman Kannywood wacce tabar baya da kura. Inda ya fada ya kuma tabbatar cewa kaf yan fim babu mai ilimin Addinin acikinsu.

Wannan magana da malam yayi tayi matukar jawo cece kuce a shafukan sada Zumunta inda Da yawa daga cikin masoyan jaruman sukaita maida martani ga malamin a karshe kuma maganar ta Matukar batawa jaruman Kannywood rai.


Dama dai wannan ba shine karo na farko ba da aka fara fadawa Jaruman irin hakan domin yawancin Malamai suna Kallon Masana’antar Kannywood ne a matsayin wani wuri daya tara wakilan shaidan dake gurbata Tarbiyyar al’umma.

Sai dai har yau jaruman Kannywood Sunki yarda da irin maganganun da malamai keyi akansu inda yawancinsu suke bayyana cewa Masana’antar su da Finafinan su suna fadakar da al’umma ba gurbata Tarbiyyar ba.


A Yanzu kuma fitaccen Malamin ya fito ya bayyana cewa dukkan Jaruman Kannywood babu me Ilimin Addini aciki kaf dinsu Jahilaine idan kuma akwai wanda yake dashi to ya fito ya bayyana.

Musbahu ya bayyana cewa aiba kai ka hallicemu ba Ko kuma zamanka mukeyi a duniya kodai jadadda mana kalamar shahada zakayi inda ya kira malamin da mahassadi Shakiyi sannan kuma Shashasha maici da Addini





0 Response to "Musbahu M Ahmad Yayiwa Sheikh Idris Abdulaziz Bauchi Zagin Kare dangi Akan Maganar da Yayi Na cewa duk Yan Fim Jahilaine"

Post a Comment