--
Yanzu yanzu Jiragen yakin Najeriya  sun yi ma yan bindiga luguden wuta a dajin Zamfara

Yanzu yanzu Jiragen yakin Najeriya sun yi ma yan bindiga luguden wuta a dajin Zamfara



Jiragen yakin Najeriya  sun yi ma yan bindiga luguden wuta a dajin Zamfara


Dakarun rundunar mayakan Sojan sama ta Najeriya sun yi amfani da jiragen yaki wajen yi ma taron yan bindigan jahar Zamfara ruwan wuta ta sama a wasu mabuyansu dake cikin dazukan jahar.


Majiyarmu ta ruwaito kaakakin rundunar Soja sama, Iya komodo Ibikunle Daramola ne ya bayyana haka, inda yace Sojojin sun kai wannan hari ne a karshen makon daya gabata bayan samun bayanan sirri dake tabbatar musu da taruwar yan bindiga a mafakokinsu.



“Sojojin dake aikin Operation Diran MIkiya sun tarwatsa wani sansanin yan bindiga da suke taruwa don tsara hare harensu a kauyen Ajia, hakan nan Sojojin sun kashe yan bindiga da dama a Ajia da Wonake, cikin karamar hukumar Birnin Magaji na jahar Zamfara.” Inji shi.


Kaakakin ya cigaba da cewa rundunar ta sake turawa da wani jirgin yakin Najeriya kirar Alpha Jet zuwa wani gida da yan bindigan suka fake a ciki, inda jirgin ya tashi gidan gaba daya ta hanyar jefa masa bamabamai, wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar yan bindiga da dama.


Cikin wani bidiyo da rundunar ta watsa a kafafen sadarwa, an hangi yadda jiragen yakin suka halaka wasu yan bindiga da suke tserewa a kafa suna neman mafaka, wasu kuma har kauyen Wanoke aka bi su kafin daga bisani aka halaka su.

0 Response to "Yanzu yanzu Jiragen yakin Najeriya sun yi ma yan bindiga luguden wuta a dajin Zamfara"

Post a Comment