--
 TIRKASHI: Akwai Yiwuwar Za'a Yanke ma Malam Abdul-Jabbar Hukuncin Kisa a Gobe Alhamis

TIRKASHI: Akwai Yiwuwar Za'a Yanke ma Malam Abdul-Jabbar Hukuncin Kisa a Gobe Alhamis

 



Cikin wata takardar da wani cikin tsoffin Lauyoyin dake tsaye ma Malam Abdul-Jabbar suka rubuta domin hutar da babban mai shari'ar dake kula da lamarij shari'ar Malamin, sun tabbatar da hukuncin kisa akan Malamin tare kuma da miƙa ma Alƙalin takardar domin ya karanta a bainar jama'a ranar Alhamis mai zuwa a matsayin hukuncin da ake sa ran yanke masa hukunci. 


👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

#https://www.facebook.com/sakona.musulunci/videos/347138600057530/?app=fbl

Sahara Reporters Hausa ta bankaɗo cewar takardar tana dauke da rubutun tabbacin furucin kalmomin da ake zargin Malamin ya furta su, kuma ya amsa furta su din kamar yanda suka bayyana.


 Kuma dukkan wanda aka zarga da furta wannan kalmomin, matukar ya amsa cewa ya furta su, to a kowane irin yanayi ya furta din hukuncin kisa za'a zartar a kansa, kamar yanda manyan Lauyoyin suka bayyana a rubuce a takardar.


Lauyoyin masu gabatar da ƙara, masana shari'a tare da haɗin Gwuiwa da daya daga cikin tsoffin Lauyan Malamin ne suka zauna suka rubuta hukuncin domin gabatar wa ga mai shari'a.


Sai dai a ɓangare guda kuma Almajiran Malam suna ta addu'ar zuwar wannan ranar tare da shirin gudanar da gagarumar zagaye a fadin Jihar ta Kano domin a cewar su a wannan ranar za'a saki Malamin nasu Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara.


#Sahara Reporters Hausa

0 Response to " TIRKASHI: Akwai Yiwuwar Za'a Yanke ma Malam Abdul-Jabbar Hukuncin Kisa a Gobe Alhamis"

Post a Comment