Yan Arewa Mu Farka: Har yanzu shafin daukar ma'aikatan Civil Defence Yana Aiki aje a cike
An fitar da sanarwar fara daukan sabbin ma'aikatan ne ta shafin yanar gizon.
Abubuwa Da Ake Bukata Don Neman Aiki A Hukumar Tsaro Ta Civil Defense A Shekarar 2022/2023.
Kazalika, hukumar tana sanar da duk masu sha'awan neman aiki cewa rajistan neman aikin kyauta ne. za a iya samun fom din a intanet kuma dukkan abin da za a yi na neman aikin a yanar gizo ne.
Jerin matakan da kowa zaibi don neman aikin Civil Defense Gasu Kamar Haka👇👇👇
1. Masu son neman aikin su ziyarci shafin hukumar
https://cdcfib.career domin karanta dukkan umurni, dokoki da abubuwan da ake bukata don neman aikin.
2. Latsa 'apply': Bayan mai neman aikin ya karanta umarnin da aka bayar a shafin yanar gizon, ana umartan shi da ya danna kan alamar APPLY don ci gaba.
3. Shigar da bayanan rayuwa: Wannan shine matakin da za a fara cike baynai gadan-gadan kuma dole a cike su yadda ya dace. Wasu daga cikin bayanan sun hada da cikakken suna, ƙasa ta asali, jinsi, lambar shaidar dan ƙasa, da wasu da dama.
4.Dora takardun shaidarka da katin shaidar dan ƙasa: A ƙarshen cike fom din, za a nemi masu neman aiki su ɗora takardar shaidar karatunsu da takardar shaidar zaman dan ƙasa.
5.Ka turo fom din neman aikin: Wannan shi ne mataki na ƙarshe. Abin da ake buƙata daga mai nema shi ne danna maɓallin aikawa bayan ya tabbatar duk bayanan da aka cika daidai ne.
6. (Maza) - 1.68m Tsawo
(Mata) - 1.65m Tsawo
Shekara - 18-30
Domin Cikewa Kai Tsaye Idan Anbude Portal Ku Latsa Adreshin Dake Kasa Mai Alamar (APPLY NOW)
Allah ya Bada Sa'a Kuyi Share Dan Allah Zuwaga 'Yanuwa Da Abokan Arziki
0 Response to "Yan Arewa Mu Farka: Har yanzu shafin daukar ma'aikatan Civil Defence Yana Aiki aje a cike"
Post a Comment