--
WANI MATASHI YAYI KIRA ZUWA GA GWAMNAN KANO ABDULLAHI GANDUJE AKAN LAMARIN SHEIKH ABDULJABBAR KABARA

WANI MATASHI YAYI KIRA ZUWA GA GWAMNAN KANO ABDULLAHI GANDUJE AKAN LAMARIN SHEIKH ABDULJABBAR KABARA

 


An ba da rahoton cewa wani Bafaranshe ya yi tattaki daga kasar Faransa zuwa Ivory Coast a yammacin Afirka don neman wata tsohuwar mata da take yi renon shi a lokacin yana jariri.


Mai renon nasa ta kasance tana kula da shi shekaru 38 da suka gabata lokacin da yake zaune a kasar Ivory Coast tare da mahaifinsa. 


Wani tsohon hoto ya nuna yadda matar ke ɗauke da Bafaranshen a bayanta lokacin yana jariri.


Sai dai a lokacin, mahaifinsa ya yi ritaya wanda hakan yasa iyalin suka bar kasar Ivory Coast, hakan yasa suka rasa saduwa da mai renon nasa. 


Shekaru 38 bayan haka, yaron, wanda yanzu ya zama mutum, ya koma kasar ta Ivory Coast don nemo matar da ta yi masa reno. 


Neman sa ya yi nasara kuma ya yi farin ciki sosai lokacin da suka sake haduwa da juna. Sun dauki hoton junan su don tattara bayanan haduwar su.


Rahotanni sun ce, Bafaranshen ya bai wa tsohuwar wasu kudi kuma ya sanya mata alawus na wata-wata da zai dinga biyanta wasu kudade.

0 Response to "WANI MATASHI YAYI KIRA ZUWA GA GWAMNAN KANO ABDULLAHI GANDUJE AKAN LAMARIN SHEIKH ABDULJABBAR KABARA "

Post a Comment