--
Muhimmiyar Sanarwa ga Dukkan Supervisor da Enumerator Wadanda zasu karbi Horo Na Musamman

Muhimmiyar Sanarwa ga Dukkan Supervisor da Enumerator Wadanda zasu karbi Horo Na Musamman


Hukumar kidaya ta kasa NPC ta fara shirya shiryen tantance sunayen Supervisor da Enumerator da zasu gudanar da karbar horo.


Na samu labari akan cewa hukumar kidaya ta canza salon yadda zata fitar da sunayen Applicant da zasu gudanar da karbar horo acikin watan june da zamu shiga na gobe .


Sanin kowa dai hukumar kidaya ta saba saka ranar karbar horo tana dagawa bisa wasu dalilai da suke shan gabanta amma in Sha Allahu zaa gudanar da karbar horo cikin watan da zamu shiga na June .


Watanin baya da suka wuce an fitar da sunaye a wasu Ƙananan hukumomi dake najeriya amma wasu basu ga sunayen su ba ! Ina so inyi amfani da wannan dama wajen sanar da mutanan da Suka bamu aikin approval an fitar da list babu sunayen su ,suyi magana ta hanyar da zaka bayar domin shigar da sunayen su in Sha Allahu .


Yanzu haka ana tantance sunayen Supervisor da Enumerator da zasu gudanar da karbar horo duk wanda sunan shi ya fito acikin list din da zaa sake zuwa gaba zai kasance cikin masu gudanar da karbar horo in Sha Allahu.


Wanda Application Status dinsu Yana Pending suma zasu iya min magana da yardar Allah zan sanar daku yadda tsarin yake za'a saka sunan ku acikin list .


Yanzu haka hukumar ta canza salon yadda zata biya ma'aikatan wucin gadin sakamakon wasu bata gari sunyi amfani da Nin number din da ba nasu ba ,Ina sanar da mutane cewa yanzu hukumar ba zatayi amfani da online sumbit bank details ba.


Yanzu kawai abu mafi mahimmanci shine sunan ka ya shiga cikin list din da hukumar zata fitar zuwa gaba.


Ranar karbar horo hukumar zata raba account fom yadda kowa zai sa account bank details dinsa da sauran bayanin sa da suka shafi ka .


Za'a cire sunayen masu irin matsalolin nan acikin list din da hukumar kidaya zata sake fitar wa 👇


❌Wanda sunayen su ya fito sau biyu acikin list .


❌Wanda yayi amfani da Nin number din da ba nashi .


❌Wanda sunan shi dake kan Profile Nin number da ban da na Npc Profile nashi.


hukumar kidaya zata cire sunayen masu matsalolin nan dana lissafo, bayanin da muka samu shine hukumar tayi haka ne saboda wasu bata gari sun yi amfani da bayanin da ba dasu ba sun shiga yanar gizon hukumar sun canza bayanin mutanan da suka samu NPC I'D Ko NIN NUMBER lokacin da ake EDITING.


Ina yiwa kowa fatan alheri.


Ahmed El-rufai Idris 

Kaduna State Coordinator Zumunta Youths Awarenesses Forum ☑️

0 Response to "Muhimmiyar Sanarwa ga Dukkan Supervisor da Enumerator Wadanda zasu karbi Horo Na Musamman"

Post a Comment