--
Anyi Kira Ga Mai Alfarma Sarkin Musulmi   Da Yasa Baki  Akan Bidiyon Wasa Da Sallah Wanda Mawaki Davido Ya Fitar

Anyi Kira Ga Mai Alfarma Sarkin Musulmi Da Yasa Baki Akan Bidiyon Wasa Da Sallah Wanda Mawaki Davido Ya Fitar


Al'ummar musulmi a Najeriya na cigaba
da tafka muharawa a kafofin sada
zumunta a kan wani faifan bidiyon da
mawaki Davido ya fitar, inda a cikin
bidiyon wakar aka hango wasu mutane
sunyi shiga irin ta musulmi tare da
kambarta sallah a wani waje mai kama
da masallaci inda mutanen suna cikin
sallar kawai suka koma tikar rawa yayin
da mai rera wakar yake kan wani gini
dake dauke da amsa kuwwar kiran sallah
yana rero wakar daga can.
Tun bayan fitar bidiyon da bai yiwa
al'ummar musulmi dadi ba, al'ummar
musulmin kasar suna cigaba da suka tare
da caccakar mawakin akan ya goge
bidiyon ko kuma ya sake gyara bidiyon ya
goge wurin da musulmin ke kallo a
matsayin raini zuwa ga addinin Islama.

Yayin da wasu kuwa ke kira ga mai
Alfarma Sarkin Musulmi da ya fito ya
kalubalanci bidiyon a fili a madadin
al'ummar musulmi kasar.

Meye ra'ayin ku kan wannan batu?

0 Response to "Anyi Kira Ga Mai Alfarma Sarkin Musulmi Da Yasa Baki Akan Bidiyon Wasa Da Sallah Wanda Mawaki Davido Ya Fitar"

Post a Comment