--
Dalilin Ciwon Baya Yayin Goyon Cikin Watannin

Dalilin Ciwon Baya Yayin Goyon Cikin Watannin


Watannin goyon ciki, musamman daga zango na biyu zuwa na uku, lokaci ne da masu juna biyu suka fi fuskantar ciwon baya ko ciwon ƙugu.

Daga cikin dalilan ciwon baya ko ciwon ƙugu ko kwankwaso yayin goyon ciki akwai sauye-sauye da suke faruwa a ƙashin baya da ƙugu sakamakon ƙaruwar nauyin ciki da kuma sinadaran haihuwa. Hakan yana haifar da ƙaruwar lanƙwasar ƙashin, sauyawar gurbin cibiyar nauyin jiki tare da juyawar ƙugu ko kwankwaso.

Bayan wannan ya faru, sai ciwon baya da ciwon ƙugu su biyo baya har zuwa lokacin haihuwa. A wasu lokutan ma ciwon yana wanzuwa har bayan haihuwar.

Sai dai, akwai haɗarin gaske ga mai juna biyu ta yi amfani da ƙwayoyin ciwon baya barkatai domin yin hakan na iya zama barazana ga lafiyarta da abin da ke cikinta.

Yana daga cikin muradan likitan fisiyo samar wa mai juna biyu sauƙi daga ciwon baya da ciwon ƙugu ba tare da shan ƙwayoyin rage ciwo ba.

Ganin likitan fisiyo yayin goyon ciki na da alfanun kiyaye ciwon baya, ƙarfafa yunƙuri yayin naƙuda da kuma kauce wa ciwon baya ko ciwo ƙugu yayin da bayan haihuwa.

Muna addu'ar Allah ya sauki masu juna biyu lafiya.

© Physiotherapy Hausa

0 Response to "Dalilin Ciwon Baya Yayin Goyon Cikin Watannin "

Post a Comment