Kungiyoyin fararen hula sun yi zanga-zangar Allah-wadai A Abuja bisa sanya sunan El-Rufai cikin ministoci
Daga Salisu Abubakar, Abuja
Da safiyar ranar Litinin 31 ga watan Yulin 2023 ne, kungiyoyin fararen hula suka gudanar da zanga-zangar Allah-wadai da sanya sunan El-Rufai cikin ministocin da gwamnatin Bola Ahmad Tinubu ta nada.
Zanga-zangar ta gudana ne a gaban majalisar kasa dake birnin Tarayya Abuja, inda masu zanga-zangar suke dauke da alluna da rubututtuka daban-daban da suke dauke da adawa da Allah-wadai da sanya sunan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai cikin jerin sunayen ministoci 28 da shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya aikawa majalisar Dattawa.
Zanga-zangar ta gudana ne a karkashin kungiyar ‘Secure Nation Group’ a karkashin ICRP.
A cikin takardar da kungiyar ta aikawa da Kakakin majalisar Tarayya wanda Kwamared Ahmad Lawal da Kwamared Emmanuel EB Godwin suka sanyawa hannu a madadin membobin kungiyar ta ‘Secure Nation Group’, kuma suka karantawa manema labarai a yayin zanga-zangar; sun bayyana cewa; “na rubuto ne domin sanar da mai girma Kakakin majalisar wakilai cewa membobin kungiyar ‘Secure Nation’ a madadin nagartattun al’ummar jihar Kaduna da Nijeriya baki daya ba su yarda da nadin Malam Nasiru El-Rufai a matsayin minista a gwamnatin Tinubu da Shetima ba.
“Abin takaici ne a ce tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai na cikin jerin sunayen ministocin da aka nada duk da dimbin zunuban da ya aikatawa al'ummar Nijeriya”, in ji sanarwar.
Kungiyar ta ci gaba da cewa; “Mai laifin da ya kamata a ce an kama shi nan take, a kuma bincike shi tare da gurfanar da shi a gaban kuliya kan kisan gillar da ya yi wa al’ummar Musulmi mabiya Shi’a a jihar Kaduna. Tantirin maƙaryaci, mai son kansa kuma shaidanin da ya damu da bukatarsa kawai.
“Yana rubuce a tarihi cewa ‘yan Nijeriya da dama ne suka gurfanar da tsohon gwamnan a kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, wato ICC, domin neman ganin an bincike shi tare da hukunta shi, idan har aka same shi da laifin kisan kiyashi da ya yi wa ‘yan Nijeriya da dama tare da lalata kadarorinsu a jihar Kaduna. Kuma a lokuta da dama, an samu Nasir El-Rufa'i da yada ra'ayoyin ta'addanci”, suka tabbatar.
Kungiyar ta ci gaba da cewa; “Tabbas, sanya sunan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai a cikin wadanda shugaba Bola Tinubu ya nada a matsayin ministoci, babban bala'i ne ga Nijeriya.
“‘Yan Nijeriya ba su manta da irin ta’asar da ya yi ba a lokacin da yake rike da mukamin Babban Darakta na hukumar lura da kadarorin gwamnati (BPE) da kuma Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja. Mutumin da ya cire ciyawa a titi daya a Abuja mai kimanin tsayin kilomita 5 da zunzurutun kudi har naira biliyan N2.1, ko shakka babu ba shi da gaskiyar da za a damka masa amanar ci gaban kasa. Barawo ne kawai.
“A matsayinsa na ministan babban birnin tarayya, kimanin mutane 800,000 ne aka kora daga gidajensu sakamakon rushe musu muhallai da El-Rufai ya yi a tsakanin shekarar 2003 zuwa 2007. Har yanzu dai ba mu manta da yadda ya kwace filaye tare da bayar da su kyauta ga ‘yan uwansa da iyalansa ba kuma ya yi ikirarin kare wannan ta’asar da cewa su ma ‘yan Najeriya ne.
“Malam Nasir El-Rufai ya bijirewa sashe na 1 na tanadin kundin tsarin mulki na biyar, wanda ya ce: jami'in gwamnati ba zai sanya kansa cikin wani yanayi da zai fifita maslaharsa a kan ayyukan al’umma ba.
“A shekarar 2021, an ruguza daruruwan gidaje a Zariya, a daidai lokacin da hukumomin jihar Kaduna suka fara wani gagarumin aikin rusa gidaje. A ranar Litinin, 22 ga Mayu, 2023 jami’an hukumar tsare-tsare da raya birane ta jihar Kaduna (KASUPDA) suka rushe wasu gine-gine a jihar.
“Gine-ginen da aka rushe sun hada da makarantu, asibiti da wasu gine-gine masu zaman kansu inda da dama suka rasa rayukansu da kuma hanyoyin neman halas dinsu. Wannan mataki ya janyo suka mai tsanani daga 'yan Najeriya da dama.
“Wasu gungun mutanen da atisayen rusau a mintunan karshe ya shafa, sune mazauna kauyen Gbagyi da ke Kaduna. Rahotanni sun nuna cewa jami’an tsaro da suke rakiyar masu rusau din sun harbi matasan da ke zanga-zangar neman hana rushe musu muhallai, inda da dama suka samu raunuka, kimanin 8 ne suka mutu. An bayyana cewa wata mazauniyar kauyen Gbagyi mai suna Sarah ta yanke jiki ta mutu a lokacin da labarin rushewar ginin ya riske ta.
A baya dai El-Rufai ya yi yunkurin rusa kauyen Gbagyi, duk da cewa kotu ta hana shi.
Wani mazaunin garin mai suna Haruna ya ce El-Rufai ya soke duk wani amincewar ginin da aka samu kafin shari’ar kotu.
“Bayan hukuncin da kotu ta yanke wanda al’ummar garin Gbagyi suka samu nasara, El-Rufai ya nemi mu cike fom domin daidaitawa a kan kudi N20,000, kuma yawancinsu sun yi hakan.
“Haka kuma, kusan kwanaki 10 da suka wuce, KASUPDA ta kawo wata takarda cewa el-Rufai ya ba da umarnin cewa duk wani amincewar gine-gine da aka samu gabanin shari’ar kotu ba su da tushe balle makama, inda ya bukaci mu fara aiwatar da sabbin amincewar gine-gine da sabbin tsare-tsare masu dauke da kwanan watan da bai wuce Mayun 2023,” aka ruwaito Haruna yana cewa.
“Me yasa irin wannan mara tausayin ne zai kasance cikin jerin ministoci a kasar da ke son kyakkyawar makoma ga al'ummarta?”, kungiyar ta tambaya.
0 Response to "Kungiyoyin fararen hula sun yi zanga-zangar Allah-wadai A Abuja bisa sanya sunan El-Rufai cikin ministoci"
Post a Comment