Ku Karanta Wannan Labarin akwai Tsantsar Darasin Rayuwa a cikinsa
NIMA KWAFOWA NAYI: Akwai Matuƙar Darasi, Nidai kam Naƙara Samun Tsantsar Imani da godiya ga Allah, akan Yanda Allah ya Bani Rayuwa da Lafiya.... Alhamdilllah 😭
Selwa Hussein Mai Rayuwa dauke da zuciyarta a bayan Jakarta
Selwa, 'yar Burtaniya, an yi mata aikin ceton rai ne a cikin 2017 bayan haka ta na dauke da zuciyarta na wucin gadi a cikin jakar ta, a baya .
Selwa Husaini ta zama mutum na biyu a Biritaniya da aka sanyawa wa zuciya ta wucin gadi. Sakamakon aikin da aka yi mata na ceton rayuwa, Selwa Hussein, mai shekaru 39, yanzu haka ta na ɗaukar zuciyarta a cikin jakar ta a bayan ta.
Kayan aikin ceton ya ƙunshi batura, injin lantarki da kuma famfo wanda ke tura iska ta cikin bututu don kunna ɗakunan robobi a cikin ƙirjinta waɗanda ke tura jini a jikinta.
Jakar ta ta, na da nauyin kilogiram bakwai kuma dole ne ta ɗauke ta a duk in da Selwa za taje awanni 24.
Ita ce mutum ta biyu a Burtaniya da za ta bar asibiti da cikakkiyar zuciya ta wucin gadi.
An kai mahaifiyar 'ya'yan biyu, daga Clayhal zuwa Asibitin Harefield, a watan Yuni tare da ciwon zuciya mai tsanani.
Ayyukan zuciyarta na tabarbarewa da sauri har likitoci su ka tilasta sanya ta a kan na'urar ECMO, na'urar ceton rai wanda ke isar da iskar oxygen daga wajen jiki tare da kula da yanayin ta.
Har zuwa shekarar 2016, Selwa ba ta da wasu alamamun ciwon zuciya, amma likitoci sun yi imanin cewa ciwon zuciya ne ya jawo sakamakon wani yanayi da ake kira familial dilated cardiomyopathy, wata cuta ta kwayoyin halitta.
Bayan ta kamu da rashin lafiya, likitoci sun ga cewa ba ta da lafiya sosai da za a yi mata dashen zuciya.
Maimakon haka, an cire zuciyarta daga jikinta kuma aka maye gurbinta da kayan aikin wucin gadi wanda likitan tiyata Diana Garcia Saez ya yi a ranar 27 ga Yuni 2017.
Ta ce: “Duk da cewa mu na ƙara ba ta magunguna, yanayin Selwa yana ƙara yin muni sosai da sauri.
"Zaɓi kawai don ceton rayuwarta shi ne ta dasa zuciya ta wucin gadi."
Bayan babban tiyatar da aka yi, Selwa ta shafe watan Agusta ta na koyan yadda ake tafiya, magana, ci da sha, a sashen da aka keɓe na Asibitin Harefield, don haɓaka ƙarfin tsoka ta hanyar jiyya.
An gudanar da aikin ne karkashin jagorancin Mista Andre Simon, darektan dashen zuciya da huhu da na'urorin taimaka wa huhu.
Ya ce: “Aikin ya yi kyau sosai kuma lafiyar Selwa ta yi kyau.
Asibitin Harefield shi ne cibiya daya tilo a Burtaniya da ke amfani da na'urar a matsayin magani ga masu fama da ciwon zuciya.
Selwa Hussein dai har yanzu ta na nan a raye, ta na cikin gaba da rayuwa da jarkarta a bayanta.
Credit:zaraddmiz katsina
0 Response to "Ku Karanta Wannan Labarin akwai Tsantsar Darasin Rayuwa a cikinsa"
Post a Comment