--
Ma'aikatar Shari'a ta jihar Kano ta musanta labarin yanke hukuncin shari'ar zaɓen gwamnan Kano

Ma'aikatar Shari'a ta jihar Kano ta musanta labarin yanke hukuncin shari'ar zaɓen gwamnan Kano



Ma'aikatar Shari'a ta jihar Kano ta musanta labarin yanke hukuncin shari'ar zaɓen gwamnan Kano a ranar Juma'a, ta ce sai nan gaba kaɗan za'a sanar da rana.

Babban mai bada Rahoto na gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, a bangaren Shari'a, wato Amir Abdullahi Kima ne ya tabbatar mana da haka, inda yace labarin da wasu ke yaɗawa na cewar kotun sauraron ƙarar zaɓen gwamnan Kano za ta yanke hukunci a ranar Juma'a ba gaskiya bane.

Kima yace har kawo yanzu ana dakon ranar da kotun zata bayyana domin yanke hukunci, harma yayi kira ga magoya bayan jam'iyyar NNPP cewa kada su tashi hankalinsu akan batun, domin duk Nigeria babu dan takarar gwamnan da ya samu ƙuri'u kamar Abba, kuma ƙuri'u halattu. 


0 Response to "Ma'aikatar Shari'a ta jihar Kano ta musanta labarin yanke hukuncin shari'ar zaɓen gwamnan Kano"

Post a Comment