--
Twitter ta biya ƴar Najeriya N245k Duba ciakken bayanin yadda ta samu da Matakan da kaima zakabi ka samu naka

Twitter ta biya ƴar Najeriya N245k Duba ciakken bayanin yadda ta samu da Matakan da kaima zakabi ka samu naka


Wata budurwa ƴar Najeriya ta samu sama da N245k a shirin raba kuɗin tallan da aka samu a Twitter wanda Elon Musk ya kawo. 


Budurwar mai suna Bamidele, ta sanya hoton ƙididdigar kuɗin da ta cancanci Twitter wacce yanzu aka sani da X, za ta biya ta.


Bamidele tana da masu bibiyarta har 102.5k, sannan ta cancanci ta samu N491k a Twitter amma a yanzu N245k kawai za ta iya cirewa


Ta bayyana cewa wannan shi ne karon farko da Twitter za ta biya ta kuɗin tun lokacin da Elon Musk ya kawo shirin a watan Yuli.


Twitter ta biya ƴar Najeriya N245k:

Masu amfani da Twitter da dama waɗanda suka ga hoton yawan kuɗin da aka biya ta, sun taya ta murna sosai. 


Domin samun damar shiga tsarin dole sai an cike wasu sharuɗɗa ciki har da samun mutum miliyan biyar waɗanda suka ga wallafar da mutum ya yi a Twitter cikin watanni uku. 


Haka kuma dole sai ya shiga tsarin Twitter Blue, kuma yana da aƙalla mabiya 500.





Majiya: Legit.ng

0 Response to "Twitter ta biya ƴar Najeriya N245k Duba ciakken bayanin yadda ta samu da Matakan da kaima zakabi ka samu naka"

Post a Comment